Shugaba Buhari ya kaddamar da sabuwar majalisar tattalin arziki ta kasa

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabuwar majalisar tattalin arziki ta kasa

A ranar Alhamis 20, ga watan Yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar majalisar tattalin arziki NEC da za ta jagoranci al'amuran kasar nan daga 2019 zuwa 2023.

Buhari ya kaddamar da sabuwar majalisar a babban dakin taro na Council Chambers dake fadar a sa ta Villa a garin Abuja.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo shi ne jagoran majalisar tattalin arziki ta kasa NEC (National Economic Council), da ta kunshi gwamnonin jihohi 36 na Najeriya.

Da yawa daga cikin gwamnonin kasar nan da suka hadar da sabbin shiga da kuma masu maimaita kujerun su, sun halarci babban taron da aka kaddamar karo na farko a wa'adin gwamnatin shugaba Buhari na biyu.

Sauran manyan kasar da suka halarci zaman sun hadar da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, babban mai bayar da shawara a kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Yayin zaman kaddamar da sabuwar majalisar a fadar sa, shugabna kasa Buhari ya gargadi gwamnonin kasar nan da su daura damarar bunkasa ci gaban kasa ta hanyar bayar da muhimmancin a fannin tattalin arziki, harkokin ilimi, tsaro, noma da kuma lafiya.

Shugaban kasar ya kuma horar da su a kan shimfida gawurtattun tsare tsare na samar da kudaden shiga a jihohin su domin inganta ci gaban al'umma da kuma kasa baki daya.

Cikin na sa jawaban, mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo, ya misalta majalisar tattalin arziki a matsayin wani ginshiki na bunkasa, bayar da shawarwari, da kuma tabbatar da tsare tsare masu nasaba da habakar tattalin arzikin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel