An gano dalilin da yasa Buhari ya sauke Baru daga shugabancin NNPC

An gano dalilin da yasa Buhari ya sauke Baru daga shugabancin NNPC

A ranar Alhamis ne kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) ta yi karin haske a kan dalilin da yasa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sauke babban darektan kamfanin, Dakta Maikantu Baru.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun Mista Ndu Ughamadu, jami'in hulda da jama'a, da NNPC ta fitar, ta ce Buhari ya canja Baru ne saboda lokacinsa ritayarsa daga aiki ya karato.

Ndu ya bayyana cewar Baru zai yi ritaya a ranar 7 ga watan Yuli bayan ya cika shekaru 60 da haihuwa.

A cewar jawabin: "shugaban NNPC, Dakta Baru, zai cigaba da jagorantar harkokin NNPC har zuwa lokacin da wa'adin yin ritayarsa zai cika a ranar 7 ga watan Yuli, 2019. Mista Mele Kolo, sabon shugaban NNPC da shugaba Buhari ya nada zai fara aiki ne a hukumance daga ranar 8 ga watan Yuli, 2019."

Kazalika, Ndu ya bayyana cewar Kyari ne ke shugabancin bangaren kasuwancin danyen man fetur a NNPC kafin shugaba Buhari ya nada shi a matsayin wanda zai maye gurbin Dakta Baru.

NNPC ta bayyana cewa bayan mukamin da ya ke rike da shi, Kyari ya kasance wakilin Najeriya a kungiyar kasahsen duniya masu arzikin man fetur (OPEC) tun 13 ga watan Mayu na shekarar 2018.

Kakakin NNPC ya bayyana cewa Kyari zai karbi shuganacin NNPC bayan ya shafe fiye da shekaru 27 yana aiki a kamfanonin kasuwancin man fetur da suka hada da kamfanin NNPC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel