Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

- An yi Lawan Shu'aibu, Shugaban jam'iyyar APC na kasa reshen yankin arewa lakabi da dan leken asirin jam'iyyar PDP

- Kwamitin Gudanarwa (NWC) na jam'iyyar APC na kasa ta jam'iyyar ne ta yi wa Shu'aibu wannan lakabin

- Kwamitin na APC ta ce PDP na sannin dukkan abinda ake tattaunawa a taron APC inda ta ce Shua'aibu ne yi wa PDP leken asiri

Kwamitin Gudanarwa (NWC) na jam'iyyar All Progressives Party (APC) na kasa ta ce Lawan Shuaibu, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, yankin arewa dan leken asiri ne na jam'iyyar PDP.

Ahmad Suleiman Wambi, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, yankin Arewa Ta Tsakiya, ya ce jam'iyyar za ta dauki mataki a kan Shuaibu kamar yadda This Day ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa Wambi ya ce: "Ina fada muku, Shuaibu ne sanadin yawancin matsalolin mu. 'Yan waje na ganin laifin Oshiomhole amma ba su san cewa Shu'aibu ne babban matsalar mu ba. Kafin mu kammala taro, PDP sun san abinda muke tattaunawa.

DUBA WANNAN: Hamshakan mata 5 da 'karan su ya kai tsaiko' a Najeriya

"Kafin mu kammala taron mu, kowa ya san matakin da za mu dauka. Ya za ayi ka gina jam'iyya tare da dan leken asiri kamar Shu'aibu a jam'iyyar ka? Amma Allah ya tona masa asiri kuma za a tona dukkan laifukansa a rahoton da za a gabatarwa kwamitin ladabtarwa."

Da ya ke tsokaci kan zargin Oyegun, jigon na APC ya ce: "Zargin da Oyegun ya yi kan Oshiomhole ra'ayoyinsa ne. Oyegun yana fushi ne saboda an sauya shi da Oshiomhole. Oshiomhole ya fi shi shiri. Yana bakin ciki ne kawai saboda an zabi Oshiomhole a maimakonsa. Ba zai taba zama kamar Oshiomhole ba."

Da ya ke mayar da martani kan zargin da ake masa na zama dan leken asirin PDP, Shuaibu ya ce: "Wa na sani a PDP da zan rika bashi bayannan sirri? Mene na yi wa PDP? Na yi wa shugaba Muhammadu Buhari kamfe a jihohin daban-daban. Saboda haka, mene ya sa za a ce ina yi wa PDP aiki?

"Bayan ganin labarin, zan tafi kotu saboda su sanar da ni aikin da na yi wa PDP. Zai zo kotu ya fada min ayyukan da na yi wa PDP. Dama shi na hannun daman Oshiomhole ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel