Har gobe ba mu yafe maku da ku ka dage zabe ba – APC ga INEC

Har gobe ba mu yafe maku da ku ka dage zabe ba – APC ga INEC

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya fito ya bayyana cewa har yanzu bai yi wa hukumar zabe na kasa watau INEC afuwa na dage zaben bana da ta yi ba a wani irin yanayi.

Adams Oshiomhole ya bayyana wannan ne a jiya Laraba, 19 ga Watan Yuni, a lokacin da ya ke maidawa INEC martani na maganar da tayi kwanaki ta bakin wani Kwamishina ta, Festus Okoye.

Har a na daf da ainihin ranar zabe, sai da Festus Okoye ya fito ya fadawa Duniya cewa INEC a shirya ta ke kan batun zaben shugaban kasa da manyan ‘yan majalisu a Ranar 65 ga Fabrairu.

A karshe dole a ka dakatar da zaben wanda hakan bai yi wa shugaban na APC na kasa da sauran mutane dadi ba. Adams Oshiomhole ya ke cewa:

“Har zuwa karfe 5:00 na yamman Ranar Juma’ar (15 ga Watan Fabriru), wasu kayan zabe su na bakin tashoshin jirgin sama. Ta ya za a dauke wannan kayan aiki zuwa Garuruwan da aka tsara a irin wannan kurarren lokaci?

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban Kamfanin NNPC

Oshiomhole ya cigaba da babatu da cewa:

“Tun da kun san cewa ba ku ida ikon jawo lokaci da sa’a 24 tun farko, da kun dauki mataki da wuri, don haka babu abin da zai sa a yi maku afuwa. A game da wannan, ban yafe maku ba.”

.".Da gan-gan ku ka jefa mu cikin wani mawuyacin hali da dole mu ka yi abin da ba mu shirya ba. Hakan (dage zabe) da ku ka yi, ya girgiza mu.”

Oshiomhole ya ce: “Ban jin cewa za ku iya kare kan ku. INEC ta tafka sakaci babba da kuma nuna tsan-tsar rashin sanin aiki. Ba za mu taba mantawa da wannan ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel