Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a kamfanin NNPC, Kyari ya zama manajan darakta

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a kamfanin NNPC, Kyari ya zama manajan darakta

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Mele Kolo Kyari a matsayin sabon Manajan Darakta na kamfanin NNPC

- Kyari wanda ya fito daga yankin arewa maso gabas zai maye gurbin Dr. Maikanti Baru

- Ya kuma nada manyan jami'an gudanarwa na kamfanin man guda bakwai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Mele Kolo Kyari a matsayin sabon Manajan Darakta na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).

Kyari wanda ya fito daga yankin arewa maso gabas zai maye gurbin Dr. Maikanti Baru.

Nadin nasa zai fara aiki daga ranar 7 ga watan Yuli 2019.

Shugaban kasar ya kuma nada sabbin shugabanin gudanarwa na kamfanin man na jiha. Sabbin jami’an sune: Mista Mr. Roland Onoriode Ewubare (kudu maso kudu); Injiniya Mustapha Yinusa Yakubu (arewa ta tsakiya), Injiniya Yusuf Usman (arewa maso gabas),; Ms. Lawrencia Nwadiabuwa Ndupu (kudu maso gabas), Mista Umar Isa Ajiya (arewa maso yamma), Injiniya Adeyemi Adetunji (kudu maso yamma),da kuma Mista Farouk Garba Said (arewa maso yamma), wadanda nadinsu zai fara aiki daga ranar 28 ga watan Yuni, 2019.

KU KARANTA KUMA: Abunda na tattauna da Buhari – Gwamnan Ogun

Shugaban kasar ya kuma yi umurnin cewa sabbin nadin suyi aiki tare da masu ci a mataki daban-daban tsakanin yanzu da ranar 7 ga watan Yuli, 2019 domin komai ya tafi yadda ya kamata a ranar 8 ga watan Yuli, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel