ACG ya tona asirin cin hancin da ke cikin aikin kwastam

ACG ya tona asirin cin hancin da ke cikin aikin kwastam

Bisa ga dukkan alamu shugabanin hukumar kiyaye fasa kwabri ta kasa kwatsam ba su jin dadin ayyukan da wasu jami'an su da ke kan iyakan kasar ke yi don hakan ya kai ga wakilin shugaban kwastam na kasa, Kwanel Hammed Ali (murabus) ya bayyana cewa wasu jami'an da ke aiki a iyakokin kasa 'ba su da amfani' saboda sun bar aikinsu sun koma yin cuwa-cuwa.

Shugaban na kwastam ya yi wannan jawabin ne a wurin taron wayar da kai da aka shirya gabanin kaddamar da shirin inganta cinikiya tsakanin Najeriya da Jamburiyar Benin.

Wakilin, Mataimakin Kwantrola Janar na Kwastam (ACG) mai kula da fannin Kimiyyar Sadarwa, Benjamin Aber ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amsa tambayoyi kan ayyukan jami'an hukumar da ke Seme border da yadda hakan ke shafan kasuwanci.

DUBA WANNAN: An bayyana kason kwamishinonin Ganduje da za su koma zango na biyu

Ya kuma lura cewa wani batu mai muhimmanci shine yadda 'yan kasuwan Najeriya ke san wahala.

Da ya ke bayar da amsa, Aber ya ce: "Tabbas wasu daga cikin jami'an mu ba su da amfani, suna barin aikinsu su koma suna wata harka ta daban kuma mu a matsayin shugabanin su ba za mu zura idanu muna kallo ba dole mu tsawatar.

"Ina tabbatar muku cewa gwamnatin Najeriya da na Jamhuriyar Benin suna kokarin kawo karshen wannan matsalan kafin ya kai mu ya baro."

Cikin fushi, Aber ya cigaba da cewa: "Mene ya sa mutanen mu ke hijira zuwa kasashen turai? Me ne zai hana mu gyara kasar mu saboda mutane su rika zuwa? Dole mu dauki matakin magance matsalolin mu."

Shugaban ya shawarci jami'an hukumar su zama masu yi wa kansu gyara a duk lokacin da suka kauce hanya domin gyaran ne zai sanya mutane su rika zuwa kasuwanci a Najeriya da Jamhuriyar Benin a maimakon zuwa kasashen turai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel