‘Yan APC da PDP da su ka sa Gbajabiamilla ya tika Bago da kasa a Majalisar Wakilai

‘Yan APC da PDP da su ka sa Gbajabiamilla ya tika Bago da kasa a Majalisar Wakilai

Shakka babu, nasarar da Femi Gbajabiamila ya samu a majalisar wakilan Najeriya, ya canza yadda ake buga siyasar kasar musamman a majalisa. Gbajabiamila wanda shi ne zabin APC, ya doke Umar Mohammed Bago a zaben.

Daily Trust ta kawo jerin wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar da su ka yi wa Femi Gbajabiamila aiki tukuru wajen ganin ya samu wannan kujera. Daga cikin su har da wasu ‘yan majalisar PDP.

1. James Faleke (APC, Legas)

Babban ‘dan majalisar na yankin Legas ya na cikin manyan na hannun daman Gbajabiamila, kuma wadanda ake tunanin cewa da su za a ci moriyar wannan majalisa saboda irin gudumuwarsa.

2. Abdulmumin Jibrin (APC, Kano)

Hon. Abdulmumin Jibrin shi ne shugaban yakin neman zaben Gbajabiamila/Wase a majalisar wakilai. Jibrin zai so ya samu babban matsayi a majalisar kasar ko ya rike kwamiti mai tsoka.

3. Alhassan Doguwa (APC, Kano)

Alhassan Ado Doguwa, wanda ba sabon-shiga bane a siyasa, ya na cikin wadanda su ka dage wajen ganin Gbajabiamila ya samu nasara. Hon. Doguwa yana harin wata babbar kujera a majalisar.

4. Ali Monguno (APC, Borno)

Ali Munguno wanda aka shirya ya zama mataimakin Gbajabiamila a 2015 ya na tare da shi har a zaben 2019. Munguno ya yi wa APC biyayya kuma ya nunawa Gbajabiamila matukar goyon baya.

5. Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa)

Razak Namdas shi ne ya kasance Mai magana da yawun bakin Majalisar Wakilan kasar a baya. Namdas ya na cikin wadanda su ka janyewa Gbajabiamila da nufin zai samu babban rabo a bana.

KU KARANTA: Aikin da ke gaban Ahmad Lawan da Gbajabiamilla a Majalisa

6. Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abia)

Hon Nkeiruka Onyejeocha ta hakura da takararta saboda Femi Gbajabiamila. Onyejeocha ita ce babbar ‘yar majalisar APC a kaf yankin Kudu maso Gabas, don haka ba mamaki ta samu mukami.

7. Linda Ikpeazu (PDP, Anambra)

Hon. Linda Ikpeazu ta na tare da Nkeiruka Onyejeocha, ko da ita ta na PDP. Hasashe na nuna cewa shugaban majalisar zai damka mata wani babban kwamiti ta rike idan an fara kason ofisoshi.

8. Beni Lar (PDP, Filato)

Honarabul Beni Lar ta na cikin sahun ‘yan a-mutun Gbajabiamila da Wase a majalisa. Wannan ‘yar majalisa ta PDP za ta tashi da wata kujera idan aka fara raba mukamai bisa dukkan alamu.

9. Olubunmi Tunji-Ojo (APC, Ondo)

Tunji Ojo ya na cikin sahun sabon shiga majalisa da su ka nuna su na bayan Femi Gbajabiamila. Shugaban sababbin ‘yan majalisar mai wakiltar jihar Ondo ba zai rasa samun sakayya ba.

10. Onofiok Luke (PDP Akwa Ibom)

Honarabul Onofik Luke shi ne ya jagoranci kamfen din Femi Gbajabiamila da Idris Wase a yankin Kudu maso Kudun da ya fito. Onofik Luke shi ne tsohon Kakakin majalisar jihar Akwa-Ibom.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel