INEC zata dauki yan bautar kasa da suka ciri tuta a zaben 2019 aiki

INEC zata dauki yan bautar kasa da suka ciri tuta a zaben 2019 aiki

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa zata dauki yan bautar kasa da suka yi aikin zaben 2019 tukuru, aiki da hukumar.

-Shugaban Hukumar, Mahmood Yakubu ne ya bayyan haka a lokacin da kungiyar EU ke kyautar da kayan aikin da tayi amfani da shi a zaben 2019

-Mahmood Yakubu ya kara da cewa aikin da yan bautar kasa ke yi ma hukumar na wucen gadi na kara taimakawa hukumar sosai

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa zata dauki yan bautar kasa da suka yi aikin zaben 2019 tukuru, aiki da hukumar, lura da yadda suka yi aiki tukuru.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan jiya a Abuja a lokacin da ake kyautar da wayoyin salula da kwamfuta wanda jami’an sa ido akan yadda aka gudanar da zaben Najeriya na 2019 na Gamayyar kasashen turai (EU) sukayi amfani da su ga yan bautar kasa 75.

Yakubu yace zaben ya yiyu ne saboda gudun muwar da yan bautar kasa su ka bayar a matsayin jami’an hukumar na wucen gadi.

“Baya ga abinda EU zata gabar yau na kyautar da wadan nan kayayyaki, hukumar zata duba rahoton zaben 2019. Akwai dayawanku dake nan da kuma wasu dayawa da basu nan, wadanda sukayi aiki mai kyau a lokacin gudanar da zaben. Zamu tantance ku za kuma mu saka ma wadanda sukayi aiki mai kyau da aiki ba tare da wasu sharudda ba. Zamu zartar da wannan daukar aiki baya ga zaben 2019, har zuwa manyan zabubbukan da zamu gudanar na zaben gwamnoni a jihar Kogi da Bayelsa a cikin watan Nuwamba.

“Na fada kuma zan kara fada cewa yan bautar kasa sune mafi jajircewa, mafi ilimi, mafi kishi kuma wadanda suke a shirye a koda yaushe don gudanar da zabe” Inji Yakubu.

KARANTA WANNAN: Shehu Sani ya fadi yadda hirarsa ta kasance da gwamnan APC da ya bar mulki

Shugaban wakilan kungiyar gamayyar kasashen turai na Najeriya, Ambasada Ketil karlsen, ya bayyana matasa a matsayin “Ginshikin dimukaradiyya saboda sune mabudin gyara gudanar da zabe a Najeriya.

"Mun fara wannan muhimmin al amari tun da dadewa. Mun so muga mun janyo matasa cikin harkar gudanar da zabe. Fiye da kashi 60 na masu zabe a Najeriya matasa ne. Saboda haka Najeriya ba zata ga cigaba ba wajen harkar dimukaradiyya har sai ta kara janyo matasa cikin al’amarin.”

Ya kara da cewa kungiyar EU ta gabatar da bincikenta game da zaben Najeriya na 2019, kuma binciken ya nuna cewa zaben, duk da bai zama mai kyau baki daya ba, akwai alamun cewa an samu ci gaba.

Babban daraktan hukumar bautar kasa (NYSC), Burgediya janaral Shuaibu Ibrahim, ya ce fiye da matasa 300,000 ake dauka cikin tsarin bautar kasar a duk shekara, kuma a wannan tsarin ana koya ma matasan abubuwa da dama ta yadda matasan zasu dogara da kansu don cigaban kansu da ma kasa baki daya.

Ya ce hadakar da akeyi tsakanin INEC da NYSC ya kara taimakawa wajen kara inganta shirin na bautar kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel