Ndume ya bukaci kotu ta soke yin amfani da kada kuri'a a sirrance

Ndume ya bukaci kotu ta soke yin amfani da kada kuri'a a sirrance

- Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa sanata Ali Ndume ya bukaci kotu ta soke yin amfani da kada kuri'a a sirrance wajen gudanar da zaben majalisa.

-Ndume ya kuma bukaci kotu da ta bayyana idan sashe na 60 na kundin tsari mulki ya baiwa wani mutum ko wani bangaren mulki damar su sauya ko gyara dokokin majalisa da tsarin mulkin ta bayan ita majalisar.

Tsohon shugaban masu rinjayen na majalisar dattawa Muhammad Ali Ndume ya bukaci babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja da ta soke matsayar da majalisar ta dauka wajen yin amfani da kada kuri'a a sirrance a zaben da ya gabata na shuwagabannin majalissar Najeriya.

A takardar shigar da karar, lauyan sanata Ndume, Gboyega Adeyenmi, ya bukaci kotun da ta bada umurni na dakatar da majalissar daga tabbatar da kada kuri'a a sirrance a matsayin tsarin zaben shuwagabannin majalissar.

A karar da ya shigar, an hada da magatakardar majalissar da kuma babban jami’in tsaro da gudanarwa na majalisar a matsayin wadanda ake tuhuma. Ndume ya musanta cewa “ Ikirarin da majalisar dattawa ta Najeriya tayi na tabbatar da yin amfani da kada kuri'a a sirrance wajen zaben shuwagabannin majalissa, ya sabawa dokokin majalissar na 2015.".

KARANTA WANNAN: Barayi ne suka sace N6.90m a gidan Zoo na Kano ba gwaggon biri ba – Manajan Darakta

Ndume ya bukaci kotun da ta zantar da hukunci akan abubuwa guda biyu wanda ya hada da bukatar kotu ta bayyana idan sashe na 60 na kundin tsarin mulki wanda ya baiwa majalisar dattawa da majalisar wakilai damar su yi dokokinsu da tsaretsaren gudanarwa su idan ya baiwa wani mutum ko wani sashe na gwamnati damar da zai canja wannan dokokin na majalisar baya ga ita majalisar.

Ya kuma bukaci kotun da tayi duba kamar haka “Duba da dokokin majalisar dattawa na 2015, wanda ya bada tsarin zabe a asirce wajen gudanar da zaben shuwagabannin majalisar, idan majalisar dattawan ba tare da gyara tsarin dokokin ba, zata iya yin amfani da budadden zabe wajen gudanar da zaben shuwagabannin majalissar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel