2019: Dalilin da ya sa ba zan shiga Kotu da Buhari ba – Kingsley Moghalu

2019: Dalilin da ya sa ba zan shiga Kotu da Buhari ba – Kingsley Moghalu

‘Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar YPP mai adawa a zaben 2019, Farfesa Kingsley Moghalu, ya bayyana abin da ya hana shi zuwa kotun saurararon karar zabe bayan kammala zaben bana.

Farfesa Kingsley Moghalu ya ke cewa an yi masa cogen kuri’a a zaben da ya gabata, amma duk da haka ba zai nufi kotu domin ya kai kara ba. Moghalu ya ce a tunaninsa hakan ne abin da ya fi dacewa.

‘Dan takarar a wajen kaddamar da wani littafi da wani babban Fasto mai suna Rabaren Dr. Owen Nwokolo ya rubuta a jihar Anambra, ya ke cewa wannan ra’ayinsa ne, kin kai kara a gaban kotu bayan zabe.

“Maganar gaskiya, shi ne ba a kirga kuri’un jama’a da kyau ba, amma duk da haka ba zan nufi kotu ba. Saboda alal-hakika zuwa kotu ba shi ba ne abin da ya fi dacewa. PDP da ta zo na biyu, ai ta tafi gaban kuliya.”

KU KARANTA: Saboda Buhari ya doke Atiku APC ta hada kai da wasu Gwamnoni

Kingsley Moghalu ya na ganin cewa duk da irin murdiyar da aka yi a zaben, zai yi wahala jam’iyyarsa ta YPP ta yi nasara a 2019. Moghalu ya nemi kotu ta yi shari’ar gaskiya a game da zaben da aka yi.

Wannan Farfesa da ya zama ‘Dan siyasa, ya kuma nemi Buhari ya karkato da akalarsa zuwa ga sha’anin tsaro da kuma tattalin arziki domin a cewarsa yanzu Najeriya ta kama hanyar sukurkucewa.

Farfesan ya tunawa Buhari cewa:

“Babban hakkin gwamnati shi ne ta kare rayukan al’umma. Talauci ya yi katutu a Najeriya, kuma duba da arzikin da Najeriya ta ke da shi, wannan abin kunya ne ainun.”

Farfesa Kingsley Moghalu ya kuma nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maza wajen nada gwamnatinsa, sannan ya yi la’akari da kwarewa da cancanta wajen zakulo Ministocin na sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel