Wata mata ta kai surukarta kotu kan ta kira ta da suna karuwa

Wata mata ta kai surukarta kotu kan ta kira ta da suna karuwa

-Hadiza Safiyanu mai shekaru 28 ta maka surukarta kara kotun musulunci a dalilin ta kira ta da suna karuwa.

-Alkalin kotun ya nemi Hadiza da ta gabatar da shaidu gaban kotun a ranar 20 ga watan Yuni kasancewar wacce ake zargin ta karyata laifin da ake zarginta da aikata wa.

Wata mata ‘yar shekara 28 ta maka surukarta kara kotu saboda ta kira ta da sunan “karuwa” a garin Rigasa dake jihar Kadunan Najeriya.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ambato cewa Hadiza Safiyanu ta shaida wa kotun shari’ar musulunci cewa ita da mijinta suna zaune a gida daya da uwar mijin tun bayan aurensu.

KU KARANTA:'Yan fashi sun kai hari gidan mai, sun kashe 'yan acaba 2 a Kaduna

Ta ce: “ Wata rana da misalin karfe 11 na dare surukata ta shigo min daki ta fara kira na da karuwa, inda take cewa in bar mata gidanta saboda mijina ya sake ni.

“ Ni kuma na ki tafiya saboda a lokacin dare ya yi. Sai ta dauko sanda ta fara dukana, yayin da ta cigaba da kira na da wasu sunayen da ba za su fadu ba.

Hadiza ta cigaba da cewa: “ Tun daga wannan lokacin na fice daga gidan, inda yanzu haka nake zaune a gidan kakana.”

Har ila yau, Hadiza ta ce, tana bukutar kotun ta tabbatar mata da sakin sannan ta debo sauran kayanta daga gidan.

Wacce ake zargin Aisha Lamido ta musanta zargin da ake yi mata. Mai shari’a Dahiru Lawal ya bai wa Hadiza umarnin ta gabatar da shaidunta a ranar 20 watan Yunin 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel