An sako Buhari a gaba a kan jan kafa wajen nada sabbin ministoci

An sako Buhari a gaba a kan jan kafa wajen nada sabbin ministoci

Reno Omokri, tsohon hadimin ga tsohon shugan kasa, Goodluck Jonathan, ya yi wa shugaba Buhari shagube a kan jan lokacin da yake yi a kan nada sabbin ministoci.

Da yake sukar Buhari a kan nadin ministocin a ranar Litinin, Omokri ya ce rashin nada ministoci a kan lokaci na daga cikin dalilan da suka sa tattalin arzikin kasa ke samun koma baya.

Shugaba Buhari ya sauke dukkan ministocinsa ranar 28 ga watan Mayu, amma har yanzu bai nada wasu sabbi ba.

Toshon hadimin shugaban kasar ya ce shugaba Buhari na zargin gwamnatin PDP a kan matsalolin tattalin arziki da kasa ke fusknata a madadin ya zargi kansa.

A wani sako da ya fitar a shafinsa na Tuwita, Omokri ya rubuta: "har yanzu shugaba Buhari bai nada majalisar zartar wa ba duk da an shafe tsawon sati uku da sake rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a karo na biyu.

DUBA WANNAN: 'Da Allah na dogara' - Atiku ya yi karin bayani a kan cewar zai jagoranci zanga-zanga

"Amma koda yaushe idan aka tambaye shi a kan dalilin tabarbarewar tattalin arzikin kasa sai ya dora laifin a kan jam'iyyar PDP da tsohon shugaban kasa Jonathan. Me zai hana mota yin hatsari idan ta hau hanya tana tafiya ba tare da direba?"

Saidai, rahotanni sun bayyana cewar shugaba Buhari zai gana da shugabnnin jam'iyyar APC na kasa da jihohi dangane da nadin sabbin ministocin.

Har yanzu babu tabbas ta fuskar su waye shugaba Buhari ke son bawa mukamin minista a zangonsa na biyu.

Tuni wasu kafafen yada labarai suka fitar da jerin sunayen wasu tsofin ministoci 12 da ake saka ran shugaba Buhari zai sake basu mukamin minista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel