Yanzu Yanzu: Buhari, Sanwo-Olu sun sa labule a fadar Shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari, Sanwo-Olu sun sa labule a fadar Shugaban kasa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun yi ganawar sirri tare da gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu

- Sanwo-Olu ya isa fadar Shugaban kasa da misalin karfe 4:10 na rana

- Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan ganawar tasu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni sun yi ganawar sirri tare da gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu.

Sanwo-Olu ya isa fadar Shugaban kasa da misalin karfe 4:10 na rana.

Ana kan ganawar a daidai lokaacin kawo wannan rahoton. Sai dai kuma babu wani Karin haske kan lamarin da za su tattauna aka.

A halin a ake ciki akwai rahotannin cewa akwai yiwuwar za a ba tsohon gwamnan jihar da ya mika wa Sanwo-Olu, Akinwumi Ambode, babban mukami na minista.

Wasu daga cikin wadannan rahoton sun kawo cewa Shugaban kasa Buhari bai ji dadin yadda babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yiwa Ambode ba a zaben fidda gwani na yan takarar gwamna a jihar.

KU KURANTA KUMA: Ganduje ya bayyana shirinsa na samar da ma’aikatar harkokin addini

“Bai ji dadi ba saboda duk da shiga lamarin da yayi, an hana wa Ambode tikitin takara a karo na biyu. Saboda haka ne yayi tunanin tausarsa,” inji majiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel