Yanzu Yanzu: Babu umurnin kotu da ya hana a binciki Sarkin Kano – Hukumar yaki da rashawa

Yanzu Yanzu: Babu umurnin kotu da ya hana a binciki Sarkin Kano – Hukumar yaki da rashawa

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tace babu wani umurnin kotu da ya hana su yin bincike aakan Sarki Sanusi

- Hukumar tace akwai dai umurni daga kotu dake kalubalantanta daga kama ma’aikatun masarautan kuma tana biyayya ga wannan umurnin

- Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimi Gado ne ya bayyana hakan

- Muhuyi ya bayyana hukumar a matsayin mai biyayya da kuma bin doka

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano tace babu wani umurni daga kotu da ya bukaci hukumar ta tsayar da bincike akan zargin kashe kudaden masarautar jihar ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tace ko da yake akwai umurni daga kotu dake kalubalantanta daga kama ma’aikatun masarautan kuma tana biyayya ga wannan umurnin.

Wannan yazo ne a wani jawabin da shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimi Gado ya yi.

Jawabin tace hukumar a matsayin mai biyayya ga doka zata cigaba da gudanar da ayyuka yanda doka ta tanadar, sannan kuma cewa tana biyayya ga umurnin kotu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo da Gbajabiamila na cikin ganawa a fadar Shugaban kasa

Ta bayyana cewa babu dokar kotu dake iya karfafa tsayar da hukuma daga daukaka hakkinta na gudanar da ayyukanta inda tayi nuni da hukunci a tsakanin Obiwusi da EFCC da ANOR (2018) LPERLR44536).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel