Lokacin da ya dace na matsa gaba yayi – Paul Pogba

Lokacin da ya dace na matsa gaba yayi – Paul Pogba

- Fitaccen dan wasan nan na Manchester United Paul Pogba, yace lokaci yayi da ya kamata ya kara gaba

- Ana sanya ran Pogba zai sauya zuwa Real Madrid ko kuma tsohuwar kulob dinsa na Juventus

- A watan Yulin 2021 ne kwantiragin dan wasan tsakiyar mai shekara 26 za ta kare

Shahararran dan wasan nan na Manchester United Paul Pogba, ya ce kakar bana ita ce ta fi dacewa da ace ya canja kungiyar wasa a cikinta.

Ana kyautata zaton Pogba zai sauya zuwa Real Madrid ko kuma tsohuwar kulob dinsa na Juventus.

Sai dai kuma a watan Yulin 2021 ne kwantiragin dan wasan tsakiyar mai shekara 26 za ta kare.

An tattaro inda Pogba ke cewa: "Ina tunanin komawa wani wurin domin tunkarar sabon kalubale.

"Shekara uku kenan ina taka rawar gani a Manchester, kuma na samu 'yan kalubale kamar yadda kowa ke fuskanta a ko'ina.

"Bayan kammala wannan kakar da irin abubuwan da suka faru, ina ganin ita ce kaka mafi kyau a gareni... ina ganin lokaci ya yi da zan matsa gaba domin fuskantar wani kalubalen."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe yan achaba 2 a Kaduna

Sai dai duk da bayanan na Pogba, wanda shi ne ya fi kowa tsada a kulob din, Manchester United sun yi imanin cewa dan wasan zai kasance a Old Trafford a badi.

A watan Afrilu, kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya ce yana sa ran Pogba zai kasance a kulob din a kaka mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel