Akwai tarin matsaloli a tsarin zaben Najeriya – Tarayyar Turai ta yi bankada

Akwai tarin matsaloli a tsarin zaben Najeriya – Tarayyar Turai ta yi bankada

- Tawagar tarayyar Turai sun bayyana cewa akwai tarin kura-kurai a gudanarwar zaben 2019 a rahoton karshe da suka saki a ranar Asabar, 15 ga watan Yuni

- Jagorar tawagar Arena tace hukumar zabe, jam’iyyun siyasa da kuma hukumomin tsaro sun hadu wajen kawo matsala a tsarin zaben na 2019

- Tawagar sun kuma soki dakatarwar da aka yi wa Alkalin alkalan kasar yan makonni kafin zaben

Rahotanni sun kawo cewa tawagar tarayyar Turai da suka sanya idanu akan zaben Najeriya da ya gabata, sun ce akwai bukatar canja tsarin zaben kasar bayan sun bankado wasu tarin matsaloli a zabukan 2019 wanda ya gudana.

Tawagar EU din sun bayyana hakan ne a yayinda suke gabatar da rahotonsu na karshe kan zaben Shugaban kasa, na yan majalisa da kuma na gwamnoni wanda aka gudanar wasu yan watanni da suka gabata.

Babbar jami'ar da ta jagoranci tawagar Maria Arena ta ce an bata gaskiyar tsarin zaben Najeriya na 2019 sakamakon rikici da barazana.

A cewarta an samu matsaloli daga bangaren tsaro, matsalar jigilar kayan zabe da kuma rashin fitowar al’umma.

Daga cikin shawarwarin da rahoton ya bayar, sun hada da inganta tsarin tattara sakamakon zabe, musamman tsarin da zai bayyanawa jama'a sakamakon kafin sanar da shi.

Babu dai wani martani da ya fito daga bangaren hukumomin Najeriya game da rahoton na Tarayyar Turai.

Rahoton na zuwa bayan watanni uku da aka gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya lashe.

Tarayyar Turai ta dora laifin matsalolin da aka samu akan jam'iyya mai mulki, kan rashin tsawatarwa ga magoya bayanta da rashin daukar matakan kaucewa cin karo da matsalolin.

Ta ce an yi amfani da karfin mulki a bangarorin Tarayya da jiha.

KU KARANTA KUMA: Wargi wuri yake samu: Shugaba Buhari ya ragargaji makarantun jami'a na kasar nan

Kuma dakatarwar da aka yi wa Alkalin alkalan kasar, makonni kafin a gudanar da zabe ya saba wa 'yancin shari'a a Najeriya.

Tarayyar Turai ta bukaci a gaggauta sauya tsarin zaben Najeriya saboda matsalolin da ta gano kafin zaben 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel