Lauyan kare hakkin bil adama ya maka gwamnatin tarayya kara kotu

Lauyan kare hakkin bil adama ya maka gwamnatin tarayya kara kotu

-Lauyan kare haqqin bil adama, Malcomn Omirhobo ya maka gwamnatin tarayya kan zancen bai wa kungiyar Miyetti Allah N100bn

-Malcomn Omirhobo ya kuma sake neman kotun ta hana Shugaba Buhari sanya dokar hana amfani da bindiga ko da kuwa tana da lasisi.

Malcomn Omirhobo, lauyan kare haqqin bil adama ya shigar da gwamnatin Najeriya kara a babbar kotun Abuja domin a dakatar da ita daga baiwa kungiyar Miyetti Allah N100bn.

Omirhobo wanda shine jagoran shigar da wannan kara a karkashin gidauniyarsa, ya nemi kotun ta hana gwamnatin tarayya bada wannan kudi kamar yadda ministan cikin gida yayi alkawari ga kungiyar.

KU KARANTA:Yadda dalibi dan shekara 33 ya zamo kakakin majalisar dokokin jihar Filato

A cikin karar da lauyan ya shigar ya ce: “ Wadannan kudade ne masu yawan gaske wanda za’a iya amfani dasu wurin yin muhimman ayyukan more rayuwa. Za’a iya bada kudin har ila yau domin taimakon masu kananan sana’o’i.”

Karar da lauyan ya shigar ta shafi gwamantin Najeriya, ministan shari’a, ministan cikin gida, sufeton yan sanda da kuma ma’ajin gwamnatin tarayya, inda take kan oda ta 3 a tsari na 6, 7 da 9 na kundin babbar kotun.

Bugu da kari, lauyan ya sake gabatar da kara kan yinkurin da Shugaba Buhari keyi domin dakatar da lasisin rike bindiga. Inda yake cewa: “ Shugaban kasa bai da wannan ikon na hana amfani da bindiga, ana rike bindiga ne domin kariyar kai.”

Jastis Ojukwu wacce ita ke sauraron shari’ar, bayan ta kamala sauraron karar da lauyan ya shigar ta ce: “ Abubuwan da kayi kara na da matukar nauyi, a don haka babu yadda za’ayi in yanke hukunci ba tare da na ji daga bangaren wadanda ake tuhuma ba.”

A karshe alkalin kotun ta dage sauraron kararrakin biyu har zuwa 30 ga watan Satumbar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel