Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Allah ya yi wa Sanata Babayo Gamawa rasuwa

Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: Allah ya yi wa Sanata Babayo Gamawa rasuwa

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na kasa, Sanata Babayo Gamawa ya rasu.

Ya rasu ne na yau Juma'a 14 ga watan Yuni a garin Bauchi bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Isah Garba Gadau, mai magana da yawun sa ya tabbatar da rasuwarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwato.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

"Ya yi koka cewa cikin sa na ciwo kuma aka tafi da shi asibitin koyarta ta Jami;ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) inda aka ba shi gado. Yanzu haka ina hanyar zuwa gidan sa," inji mai magana da yawun sa.

Kafin rasuwarsa, Sanata Gamawa ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC kafin zaben 2019 bayan jam'iyyar PDP ta dakatar da shi.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.

Tsohon dan siyasan ya taba zama kakakin majalisar jihar Bauchi a lokacin mulkin tsohon gwamna Isa Yuguda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel