Buhari ya taya Abdulsalami Abubakar murnar cika shekaru 77 da haihuwa

Buhari ya taya Abdulsalami Abubakar murnar cika shekaru 77 da haihuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a ya mika sakon taya murnar da tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Abdulsalami Abubakar kan cika shekaru 77 da haihuwa.

Ya taya shi murna kan rayuwa da ya yi mai amfani da yi wa kasa hidama da taimakon al'umma.

Sakon shugaban kasan na dauke ne cikin jawabin da hadiminsa na fannn kafafen yada labarai, Garba Shehu ya fitar a Abuja.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

Abdulsalami Abubakar ya yi mulkin Najeriya daga ranar 8 na Yunin 1998 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 1999.

Ya yabawa tsohon shugaban na Najeriya kan kokarin da ya yi na tabbatar da zaman lafiya da kawo cigaba a Najeriya da Afirka.

A cewar Buhari, tsarin mulkin Abubakar na rashin son kai da tafiya tare da matasa ya banbanta shi da sauran shugabanni. Ya kuma yaba masa saboda mika mulki ga gwamnatin faran hula a shekarar 1999.

Ya yi addu'a Allah ya cigaba da bawa Mista Abubakar tsawon rai da lafiya a yayin da ya ke cigaba da yi wa al'umma hidima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel