Cikin ruwan sanyi zan sake lashe zaben gwamna a karo na biyu – Yahaya Bello

Cikin ruwan sanyi zan sake lashe zaben gwamna a karo na biyu – Yahaya Bello

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa baya hana idonsa bacci kan nasarar zabensa a karo na biyu wanda za a gudanar a watan Nuwamba

- Bello yace cikin ruwan sanyi zai lashe zaben jihar a karo na biyu

- A cewarsa shine ya sake gina APC a jihar don haka batun samun tikiti ba wani abu mai wahala bane

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni ya kaddamar da cewa baya hana idonsa bacci kan nasarar zabensa a karo na biyu wanda za a gudanar a watan Nuwamba.

A cewarsa, cikin ruwan sanyi zai yi naasarar zaben da tazara mai yawa.

Yayi magana ne ga manema labarai na fadar Shugaban kasa bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Yae: “Nine Gwamna yau kuma in Shaa Allah, zan dawo a matsayin gwamna na wasu shekaru hudu masu zuwa, bayan zaben ranar 16 ga watan Nuwamba.

“Akan batun tikitin kuma, abun shine dan haya ba zai iya korar maigida daga gidansa ba. Don haka, ni na sake gina APC a jihar Kogi, bayan kyakyawar aikin da marigayi shugabanmu nagari, Mai girma, Prince Abubakar Audu yayi.

“Bayan rasuwarsa, na zo, na sake gina ta zuwa yadda take a yau. Wannan ce hujja a fitar jam’iyyar na karshe inda jam’iyyar inda muka samu 25/25, a majalisar dokokin jihar.

“Mun kuma samu kujeru 7 cikin 9 a majalisar wakilai sannan biyu daga cikin kujerun sanatoci uku da ke wakiltan jihar Kogi a majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Za a gabatar da kasafin kudi cikin wata 3 – Shugaban majalisar dattawa

“Saboda haka duk wanda ke irin wannan hayaniya, baya damuna, saboda a kasuwa, hayaniya abun yi ne. Kun sani, siyasar Kogi ta kasance mafi zafi, don haka dole mutane su yihayaniya kuma ba za a iya hana hakan ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel