Buhari ya umurci CBN da su sa ido akan masu shigowa da Manja

Buhari ya umurci CBN da su sa ido akan masu shigowa da Manja

- CBN zasu janye tallafi daga masu shigowa da manja daga kasahen waje

- Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefele ya bayyana cewa shugaban kasa ya bada umurni da a tallafa masu tatso manja a Najeriya

- Wannan umurni na da zummar hana shigowa da kayan da muke da su a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci babban bankin Najeriya (CBN) da su cire sunan duk wani kamfanin da aka samu da hannu wajen shigowa da manja daga jadawalin bankin.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefele ne ya bayyana haka yau Jum'a 14 ga watan Mayu a lokacin da yake ganawa da masu tatso manja a Abuja.

Emefele ya bayyana cewa shugaban kasa ya bada umurni ga babban banki da ya tallafama kamfanoni da mutanen dake tatso manja da kuma wasu abubuwa guda 10 a Najeriya.

KARANTA WANNAN: An shiga rudani yayinda tsawa ta sauka a ofishin yan sanda a Wukari, Taraba

Sauran Abubuwan sun hada da shinkafa, masara, rogo, tumatur, adduga, man gyada kiwan kaji, kiwan kifi, kiwon dabbobi na madara da kuma kadanya.

Tun bayan hawan shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2015, ya dakatar da shigowa da wasu kayan abinci daga kasashen waje.

A cikin shekarar 2016, gwamnatin ta hana shigowa da wasu kayayyakin abinci, wanda mai magana da yawun ministirin kudi Festus Akanbi a lokacin ya bayyan su. sun hada da:

1. Tsuntsaye masu rai ko danyu

2. Naman Alade da na Shanu

3.kwayayen kaji

4.Man gyada

5. Fulawa

6. Sukari

7. Tariya

8. Lemun gwangwani da na roba

9. Ruwan roba

Dukkan wadannan kayan da aka hana shigowa dasu daga kasashen ketare za a rinka bada tallafi ga duk wanda ke da sha'awar yayi kasuwancinsu cikin gida. Haka zalika wadanda dama suna cikin harkar za a tallafa masu.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel