Tirkashi: Na yiwa mahaifiyata fyade ne saboda na kasa boye sha'awata - Wani dan shekara 40 ya koka

Tirkashi: Na yiwa mahaifiyata fyade ne saboda na kasa boye sha'awata - Wani dan shekara 40 ya koka

- An cafke wani mutumi da ya yiwa mahaifiyarsa fyade

- Yayi amfani da bindiga ne wurin tsorata mahaifiyar tasa

- Daga karshe matasan unguwar sun mika shi gurin jami'an NSCDC

Jami'an hukumar Civil Defence sun cafke wani mutumi mai suna Paul Ihuaka, mai shekaru 45 da laifin yiwa mahaifiyarsa fyade.

Ihuaka, wanda dan asalin garin Umueke Ezagbogu ne, wanda ke cikin karamar hukumar Ezinihitte Mbaise dake jihar Imo, wasu matasa ne suka kamashi suka danka shi a hannun hukumar, bayan mahaifiyar tasa ta kai musu rahoton abinda ya faru.

Kwamadan hukumar NSCDC ya bayyana cewa: "Jami'an hukumar sun je har gidan mutumin da ake zargin suka kama shi."

A lokacin da manema labarai suke tambayar wanda ake zargin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa lokacin ya sha giya ya bugu ne.

KU KARANTA: Ga irin ta nan: Amurka ta jefa kasar Saudiyya cikin tsaka mai wuya

"Bayan na sha giya na bugu, sai naji sha'awa ta taso mini sosai kuma na kasa danne sha'awar tawa, sai nayi amfani da wata karamar bindiga na tsorata mahaifiya ta bani kanta na kwanta da ita," in ji Ihuaka.

Da aka tambayeshi ko yayi aure, mai laifin ya bayyana cewa bashi da halin yin aure tunda har yanzu babu aikin da yake yi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru a gidan mai laifin inda yake zaune tare da mahaifiyar tasa.

Mahaifiyar wacce ta bukaci a boye sunanta ta bayyana cewa wannan shine karo na biyu da lamarin ya faru.

Ta ce: "Ina tsakar dafa abinci sai na ganshi ya shigo da bindiga a hannunsa. Ya tsorata ni da ita, ya ce zai kashe idan har ban bashi hadin kai ba. Babu abinda na iya a lokacin sai rokonshi nake akan yayi haquri ya ajiye bindigar.

"Muna haka ne ya takura ni har yayi amfani dani.

"Dole yasa na kira matasan unguwar mu da safe, saboda lokacin da lamarin ya faru dare yayi sosai. Daga nan matasan suka je ofishin jami'an tsaron aka zo aka kamashi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel