Ga irin ta nan: Amurka ta jefa kasar Saudiyya cikin tsaka mai wuya

Ga irin ta nan: Amurka ta jefa kasar Saudiyya cikin tsaka mai wuya

- Amurka za ta gabatar da kudurin daina sayarwa da kasar Saudiyya da sauran kasashen Gabas ta tsakiya makamai

- Wani dan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrats ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar

Dan majalisar wakilan kasar Amurka na babbar jam'iyya mai mulki ta Democrats, Ted Lieu ya gabatar da wani kuduri a gaban majalisar wakilan don neman kawo hanyar da za a kawo karshen sayarwa da kasar Saudiyya makamai daga kasar Amurka.

Sanarwar ta fito daga ofishin kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar, wanda dan majalisar birnin California Ted Lieu ya gabatar da kudurin a gaban shugaban kasar Donald Trump domin ya dakatar da saida wa kasar Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf makamai.

KU KARANTA: Wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani dangane da matar shugaban kasa Aisha Buhari

Sanarwar da dan majalisa Lieu ya gabatar ta ce, a dokar sayar da makamai na kasar Amurka ana duba amfanin da kasar da za a sayarwa makamin zai yi mata, sannan kuma sai an nemi amincewar majalisar dokokin kasar, amma kuma gwamnatin Trump ba ta amfani da wannan dokar kawai sai ta ke yin gamon kanta.

'Yan majalisar wakilai na babbar jam'iyyar Democrats mai mulki Abigail Spanberger, Tom Malinowski da David Cicilline sun gabatar da kudurin sayar da makamai masu linzami a ake iya sarrafasu daga nesa.

Ranar 24 ga watan Mayu ne shugaban kasa Donald Trump ya amince da a sayarwa kasar Saudiyya da wasu manyan kasashe na yankin gabas ta tsakiya makamai ta hanyar amfani da dokar neman amincewar majalisar kasa.Saboda haka ne yasa Trump ba zai nemi amincewar majalisar kasar Amurka ba, inda Amurka za ta sayar da makamai na dala biliyan 8 da miliyan 22 ga kasashen Gabas ta Tsakiya.

Kasar Amurka dai tayi kaurin suna wurin sayar da makamai ga kasashen duniya, musamman kasashen da suke fama da barazanar yaki da kuma kasashen da suke fama da 'yan ta'adda.

Kasashen da suke sayen makaman sun hada da kasar Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da masu manyan kasashen Gabas ta tsakiya.

Haka a yankin nahiyar Afirka kasar Najeriya ta yi kaurin suna wurin sayen makamai daga wurin kasar ta Saudiyya.

Rahotanni sun nuna cewa kasar Amurkan ta bayyana cewa har yanzu babu zancen sulhu tsakaninta da kasar Iran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel