An gano jaririyar da aka sace a asibitin Jos

An gano jaririyar da aka sace a asibitin Jos

-An gano waya jaririya da aka sace bayan kwana uku da haihuwarta

-An gano jaririyar ne bayan da yan sanda suka shiga bincike, daga karshe suka damke matar da ta sace ta

-Gwamnan jihar Plateau, inda abun ya afku, ya ce za a dauki mataki ta yadda hakan ba zai sake faruwa ba

Shugaban asibitin kwararru na jihar Plateau, Dr Philemon Golwa ya ce an samu gano jaririyar da aka sace kwana ukuk da haihurta kuma tana samun kulawa ta musamman a asibitin.

Ya ce an samu gano jaririyar ne bayan da mahaifiyar jarirriyar ta ta tabbatar da kaman ninta. Jaririyar na samun kulawa ta musamman.

"Mahaifiyar jaririyar ta gane jaririnta kuma mun samu nasarar kwato ta daga hannun wacce ta sace ta kuma yanzu haka tana samun kulawa ta musamman daga kwararrun malaman jinya."

An sace jaririyar ne daga wajen mahaifiyarta mai suna Chuwebuka Zarmaganda mai shekaru 30 bayan kwana uku da haihuwarta a asibitin da ta haihu.

KARANTA WANNAN: An shiga rudani yayinda tsawa ta sauka a ofishin yan sanda a Wukari, Taraba

Mahaifiyar ta bayyana ma manema labarai cewa an ta haifi jaririyar a ranar 28 ga watan Mayu 2019 amma wata wadda tayi shigar likitoci ta sace ta a ranar 31 ga watan Mayu.

" Nazo asibitin a ranar Litinin amma na haihu a da safiyar lahadi misalin karfe 3:45."

"Na zubar da jini sosai wajen haihuwar wanda hakan ya sanya dole sai an yi mani karin jini gashi kuma mijina baya nan, dole saide na kira mahaifiyata."

"Anyi mani karin jini tun daga ranar Laraba har zuwa ranar Juma'a. Ya kamata ace an sallameni a ranar Juma'ar amma likita yazo ya ce akwai sauran abinda za a yi mani washe gari"

"Da misalin karfe 6:17 na yamma, sai wata mata tazo da kayan likitoci a jikinta tace in bata takarda ta, sai na bata takardar da likita ya bani amma sai tace ba ita take bukata ba ta jaririyata take bukata."

"Babu kaya a jikin jaririyar tawa amma sai tace lallai lallai sai an sanya mata kaya saboda zata tafi da ita dakin jarirai, ta kuma ce mahaifiyata ta biyo ta." a bayanin ta

Tace da ta lura an sace mata jaririyarta ne tayi maza ta gayama malaman asibitin.

Gwamnan jihar ta Plateau Simon Lalong wanda yaje asibitin da abun ya faru ya ce yan sanda na cikin bincike ya kuma bukaci mai jinyar da kada ta yanke kauna.

Ya kuma ce za a sanya matakai don ganin an magance sake afkuwar lamarin.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sanda ta jihar, Terna Tyopa ya ce yan sanda sun dukufa wajen bincike wanda daga bisani suka samu labari cewa wata mata mai suna Leritshimwa Diyal yar karamar hukumar Jos ta kudu na ikirarin ta haihu a ranar 31 ga watan Mayu a lokacin tana hannun yan garkuwa da mutane

Ya ce daganan sai matar ta kai jaririyar asibitin koyarwa na jami'ar Bingham don a duba jaririyar.

Jami'in ya ce yanzu matar na a hannun hukumar kuma tana bada hadin kai wajen ci gaba da binciken da sukeyi.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel