Buhari da Gwamna Bello sun saka labule a fadar gwamnatin Najeriya

Buhari da Gwamna Bello sun saka labule a fadar gwamnatin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a fadarsa da ke Abuja a ranar Juma'a 14 ga watan Yunin 2019.

Gwamna Bello ya ki bayyana abinda ya tattauna da shugaban kasar amma ya sha alwashin cewa zai koma kan karagan mulki zango na biyu.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta zabi ranar 16 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa.

DUBA WANNAN: Assha: 'Yar majalisa ta sha mari a hannun abokin aikin ta

Gwamnan ya yi watsi da hasashen da wasu ke yi na cewa ba zai samu tikitin takarar gwamna ba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) saboda rikicin cikin gida da ke faruwa a jiharsa.

"Ni ne gwamna a yanzu kuma da izinin Allah zan cigaba da zama gwamna na wasu shekaru hudu bayan zaben ranar 16 ga watan Nuwamba."

A kan batun tikitin takarar zabe kuma, zancen shine dan haya ba zai iya korar mai gida daga gidansa ba.

"Ni ne na gina jam'iyyar APC a Kogi bayan aikin da tsohon marigayi Alhaji Abubakar Audu ya yi. Bayan rasuwarsa, ni ne na sake gina jam'iyyar har ta kai matsayin ta na yanzu.

"Kowa na iya ganin hakan a zaben da ta gabata inda muka samu kujeru 25 cikin 25 na Majalisar Dokoki na Jiha. Mun kuma lashe kujeru 7 cikin 9 na Majalisar Wakilan Tarayya da kuma biyu cikin uku na Majalisar Dattawa."

Bello ya ce yana da tabbas cewa shine zai lashe zaben cikin gida na APC da ma kujerar gwamna a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba.

"Ina da danganta mai kyau da 'yan jam'iyya ta tun daga kananan hukumomi zuwa mataki na kasa. Sun san ni ne jagoran jam'iyyar mu a jiha ta.

"Batun zaben Gwamna na watan Nuwamba, ba maganan cin zabe a keyi ba, maganar irin tazarar da za mu bawa abokan hammayar mu a keyi. Tazarar da za mu ba su zai sanya ba za su samu kwarin gwiwan zuwa kotu ba," inji Bello.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel