Jami'ar Abuja zata karrama dalibai 24 da suka samu lambar farko a matakin digiri

Jami'ar Abuja zata karrama dalibai 24 da suka samu lambar farko a matakin digiri

-Jami'ar Abuja za tayi bikin yaye dalibanta karo na 23 inda zata karrama dalibai 24 wadanda suka yi nasarar kammala karatun digiri da matakin farko na fes kilas.

-Shugaban jami'ar Farfesa Micheal Adikwu ne ya bayyana wannan labari ga 'yan jarida yayin wani taro da akayi kafin bikin yaye daliban wanda zai zo ranar Asabar a jami'ar.

Dalibai 24 cikin 5,288 da za’a yaye a bikin yaye dalibai karo na 23 na Jami’ar Abuja wanda za ayi ranar Asabar za su karbi digiri mai matakin ‘fes kilas’.

Da yake tsokaci a kan wani taro da aka shirya gabanin babban tarion yaye daliban, shugaban jami’ar, Farfesa Micheal Adikwu ya ce: “ Jami’ar zata yaye dalibai masu wadanda suka kammala karatun digiri na farko da kuma wadanda su kayi na biyu da na uku.”

KU KARANTA:Talauci ne ke kawo tashin hankali a kasarmu, inji Buhari

Shugaban jami’ar ya cigaba da cewa: “ A ranar bikin zamu basu shahadarsu ba tare da je ka kadawo ba, domin sauwake masu zirga-zirga.”

“ Dalibai 4,946 ne za’a ba shahadar digiri inda kuma dalibai 342 zasu karbi shahadar mataki na gaba da digiri.”

“ Dalibai 24 ne suka samu nasarar samun mataki na farko wato fes kilas, 982 kuma suka ciyo daraja mai bi ma na farkon sai kuma 2,498 da suka ci mataki na uku, 1,085 suka ci matakin kusa da na karshe sai 137 wadanda suka zo a matakin karshe.”

“ Akwai dalibai 68 wadanda suka kammala karatun digiri na uku mai matakin Dakta, sai kuma dalibai 233 masu kammala digiri na biyu da kuma dalibai 41 masu yin babbar difuloma.” Kamar yadda shugaban jami’ar ya fadi.

“Mun shirya tsaf domin ba dukkanin dalibanmu shahadarsu, kuma wadanda suka kammala da matakin farko na fes kilas zamu karramasu na musamman.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel