Ku yi watsi da jerin sunayen ministocin Buhari na bogi da ke yawo – Fadar Shugaban kasa

Ku yi watsi da jerin sunayen ministocin Buhari na bogi da ke yawo – Fadar Shugaban kasa

- Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da wasu jerin sunaye da ke yawo a matsayin na sabbin ministocin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada

- Tolu Ogunlesi, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da duk wani bayani da bai fito kai tsaye daga fadar shugaban kasar ba

- Ogunlesi ya bayana hakan ne a shafinsana Twitter

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da wasu jerin sunaye da ke yawo a matsayin na sabbin ministocin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada.

Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a shafukan zamani, Tolu Ogunlesi, ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da sunayen a wani rubutu da ya wallafa a shafisa na twitter, @toluogunlesi.

Ga fassarar abunda ya rubuta a shafin nasa da Hausa:

“Mutanen shafukan zumunta sun fara watsa fayil din Next Level, LOL.

“Ku yi watsi da du wani bayani da ba a sanar kai tsaye daga fadar Shugaban kasa ba. Ba a nada mutane a shafin WhatsApp ko Facebook ba.

“Idan kana fama da gajiya sannan kana bukatar nishadi, ka jira BBN. Nagode,” inji shi.

A baya Legit.g ta rahoto cewa ministocin Buhari sun kara kaimi wajen matsin lamba da kamun kafa a wurin makusanta shugaba Buhari domin a sake koma wa gwamnati da su.

Rahotanni sun bayyana cewar a kalla kaso 70% na ministocin Buhari sun bar aiyukan su domin cigaba da shige-da-ficen ganin sun samu koma wa kujerun su.

Sai dai wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar ministocin sun shiga kamun kafa ne saboda sun san cewar wannan karon shugaba Buhari ba zai dauki dogon lokaci ba wajen nada ministocin da zasu taya shi aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel