NDLEA ta gurfanar da mutum biyu a bisa zargin safarar kilo 2,139 na tabar wiwi

NDLEA ta gurfanar da mutum biyu a bisa zargin safarar kilo 2,139 na tabar wiwi

-NDLEA ta gurfanar da Michael Ifeakachu da Alex Adibeli a gaban watta babbar kotu a jihar Legas

- Ana zarginus da shigowa da tabar wiwi mai nauyin kilo 2,139

- Kotu ta bayar da belinsu akan kudi Naira miliyan 10

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta gurfanar da mutum biyu a gaban Babban kotun gwamnatin tarayya dake Legas bisa zarginsu da safara tabar wiwi mai nauyin kilo 2,139.

Alex Adibeli dan shekara 43 da Michael Ifeakachu dan shekara 46 sune ake zargi da laifin shigowa da tabar.

Lauyan NDLEA, Jeremiah Aerna na tuhumar wadanda ake zargin da cewa sun aikata laifin a ranar 3 ga watan Mayu 2019 a jihar Legas.

Aerna ya ce sun hada kai ne inda suka shigo da tabar wiwin mai nauyin kilo 2,139 a boye a cikin babbar mota ta yadda baza a gane su ba.

Ya ce a bisa rahoton da suka samu ne jami'an hukumar suka gano tabar wiwin da aka boye a cikin babbar motar.

Ya ce laifin ya sabawa sashe na 11(b) da 14(b) na dokar NDLEA.

Wadanda ake zargi da laifin sun musanta zargin da ake tuhumarsu da shi. Bayan da suka musanta zargin da ake masu, lauyan su Benson Ndakara ya roki kotu da ta bada belin su.

KARANTA WANNAN :Wata kungiya ta bukaci a binciki Obasanjo da Jonathan

Daga bisani mai shari'a Salisu Sa'idu ya bada belin su akan kudi Naira miliyan 10 da kuma mutum biyu da zasu tsaya masu suma akan kudi Naira miliyan goma goma.

Alkalin ya ce dole ya kasance mutanen da zasu tsaya ma masu laifin sun mallaki filaye ko gidaje a inda kotun take da iko kuma sai sun kawo jinginar takardun filayen ko gidajen.

Daga bisani Alkalin ya dage shari'ar zuwa 24 ga watan Oktoba 2019 don ci gaba da sauraren karar.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel