Wata kungiyar arewacin Najeriya ta nuna amincewarta da jagorancin Lawan da Femi

Wata kungiyar arewacin Najeriya ta nuna amincewarta da jagorancin Lawan da Femi

-Kungiyar matasan arewacin Najeriya ta bayyana Lawan Ahmad da Femi Gbajabiamila a matsayin mutane biyun da suka dace da rike kambun jagorancin majalisar dokoki a daidai wannan lokaci.

-Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar ne ya bada wannan jawabi yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kaduna.

-Shugaban matasan ya sake bayyana cewa matasan arewa na nan na jiran ganin canji daga bangaren majalisar dokoki saboda samun wadannan jajirtattun mutane da majalisar tayi.

Gamayyar kungiyar matasan arewa ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Lawan Ahmad da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin zabi nagari ga ‘yan Najeriya.

Kungiyar har ila yau, ta taya sanata Ovie Omo-Agege tare da Hon. Ahmad Idris Wase murnar kasancewa mataimakan shugabannin majalisun biyu.

KU KARANTA:Gbajabiamila ya gargadi magatakardar majalisa yayinda batatun lasifiku suka kawo tsaiko a zaman farko

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, shugaban kungiyar, Murtala Abubakar ya ce: “A halin yanzu da aka riga aka kammala zabe, muna sa ran ganin canji daga bangaren majalisar dokoki.”

Murtala ya ce: “Kungiyarsu na tare da sabbin shugabannin majalisar dokokin dari bisa dari, kuma zasu bada gudumawarsu daidai gwargwado domin ganin an samu abinda ake nema na cigaba.”

“Ko shakka babu jagorancin majalisa abin so ne ga ko wane dan majalisa. Sai dai kuma Allah ya riga ya zabi wadanda yake so, don haka nake rokon wadanda ba suyi nasara ba da su zo a gudu tare a tsira tare domin cigaban kasarmu.”

“ Bamu da tantanma ko kadan a kan sabbin jagororin majalisar, duba ga kwarewarsu a bangaren aikin majalisa mun san ba zaben tumun dare a kayi ba, tabbas ‘yan Najeriya za suyi na’am da wadannan mutane.” Inji shugaban kungiyar matasan.

Bugu da kari, yayin da shugaban ke cigaba da yaba ma shugabannin majalisar dokokin, Murtala ya ce: “Dukkanin yan majalisar sunyi abin a yaba masu musamman yadda suka ajiye banbancin jam’iya gefe su kayi zabe cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel