Za a gabatar da kasafin kudi cikin wata 3 – Shugaban majalisar dattawa

Za a gabatar da kasafin kudi cikin wata 3 – Shugaban majalisar dattawa

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yace a karkashin mulkinsa, za a gabatar da kasafin kudin kasar na shekara-shekara cikin wata uku

- Lawan ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa

- Yace idan aka mika kasafin kudin a kashen watan Satumba ko farkon watan Oktoba, toh za a duba sannan a gabatar ashi kafin hutun Disamba

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni yace karkashin mulkinsa, za a gabatar da kasafin kudin kasar na shekara-shekara cikin wata uku.

Da yake Magana bayan idar da sallar Juma’a a fadar Shugaban kasa, Lawan yace domin cimma wannan nufi, ya zama dole bangaren zartarwa da na dokoki suyi aiki tare cikin mutunci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a karkashin tsohon shugaban majalisar datawa, Bukola Saraki kasafin kudin kasar ya kwashe tsakanin wata shida da bakwai kafin a gabatar da shi a majalisar dokokin tarayya.

Lawan wanda aka zaba a matsayin Shugaban majalisar dattawa a ranar Talata, 11 ga watan Yuni, yace za a duba sannan a gabatar da kasafin kudin cikin wata uku.

Yace idan aka mika kasafin kudin a kashen watan Satumba ko farkon watan Oktoba, toh za a duba sannan a gabatar ashi kafin hutun Disamba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu tayi watsi da bukatar mahukuntan fadar Kano na ruguje sabbin masarautun jihar

Yace za a ware wata guda domin tattauna kasafin kudin a tsakanin shugabannin hukumomi. Yace ba zai lamunci kowani jinkiri daga gare su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel