Kungiyar Igbo ta roki Buhari ya nada sakataren tarayya daga bangarensu

Kungiyar Igbo ta roki Buhari ya nada sakataren tarayya daga bangarensu

-Kungiyar kabilar Igbo na rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bada kujerar sakataren gwamnatin tarayya zuwa ga yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

-Shugaban kungiyar ta inyamurai mai suna Igbo Amaka ne ya yi wannan kiran a ranar juma'a a babban birnin jihar Ebonyi yayin wata zantawa da manema labarai.

Wata kungiyar inyamurai mai suna Igbo Amaka (AM) ta roki Shugaba Buhari da ya ba yankin Kudu maso Gabas kujerar sakataren gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar Micheal Okoro shi ne ya bayyanawa manema labarai wannan koken nasu ranar Juma’a a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.

KU KARANTA:Rashawa: Kotu ta dage sauraron karar Jonah Jang har zuwa 27 ga watan Yuni

Kungiyar ya bayyana cewa, “ Kabilar Igbo ta dade ta na bayar da gudumawa domin cigaban Najeriya. Inda ta cigaba da cewa wariyar da ake nuna wa yankin nasu sam bai kamata ba.”

Okoro ya cigaba da cewa: “ Duk da irin gudumuwar da yankin na Igbo ke badawa, abin mamaki babu su cikin wadanda suke rike da mukamai a wannan gwamnatin.”

Bugu da kari, ya sake janyo hankali zuwa abinda akayi na ware kabilar Igbo daga cikin rabon mukamai na sabuwar majalisar dokoki ta 9 wacce aka kaddamar kwanan nan.

Shugaban ya sake cewa: “ Mun yadda cewa ganawa tana samar da maslaha a irin wadannan matsaloli. Ya kuma yi amfani da wannan damar domin janyo hankalin yan yankin nasu dasu nemi ganawa da Buhari a kan wannan matsalar.”

“ Ba abu bane wanda yake a boye, kowa ya san an manta da Igbo a cikin lamuran mulkin kasar nan. A matsayinmu na kungiya wace keda kyakkyawan zato ga shugaban kasa muna sa ran zai share hawayenmu ya baiwa kabilarmu kujerar sakataren gwamnatin tarayya.” A cewar Okoro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel