An shiga rudani yayinda tsawa ta sauka a ofishin yan sanda a Wukari, Taraba

An shiga rudani yayinda tsawa ta sauka a ofishin yan sanda a Wukari, Taraba

- Tsawa ta sauka a ofishin yan sanda a Wukari, yaayinda aka zuba ruwan sama kamar dab akin kwarya a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni

- Tsawar ta tuge wani babban bisiya a gaban ofishin yan sandan yayinda tayi rugu-rugu da shi

- A cewar wani jami’i, ba a rasa rai ko dukiya ba a yayinda lamarin ya afku

Jami'an Ofishin yan sanda a Wukari, jihar Taraba sun shiga tashin hankali a lokacin da ruwan sama mai karfi ya zuba a daren ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni.

Koda dai babu wanda ya jikkata, wani babban bishiya da ke gaban ofishin yan sanda ya tugo sannan tsawa tayi rugu-rugu dashi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wasu jami’an yan sanda da ke bakin aiki a lokacin da tsawar ta sauka sunce karar ta ya razana su sosai inda dukkansu suka nemi wajen buya.

Wakilin Daily Trust da ya ziyarci wajen a Wukari ya ga yadda tsawar ta rugurguza bishiyan zuwa kanana.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu tayi watsi da bukatar mahukuntan fadar Kano na ruguje sabbin masarautun jihar

Wani jami’in dan sanda wanda ya nemi a boye sunasa yace babu wani mutum ko abun hawa da ke karkashin bishiyan a lokacin da tsawar ta sauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel