Yanzu Yanzu: Kotu tayi watsi da bukatar mahukuntan fadar Kano na ruguje sabbin masarautun jihar

Yanzu Yanzu: Kotu tayi watsi da bukatar mahukuntan fadar Kano na ruguje sabbin masarautun jihar

- Babbar kotun jihar Kano tayi watsi da bukatar mahukuntan fadar jihar na dakatar sabbin sarakuna

- Justis Ahmed Tijani Gbadamasi na kotun ya yi watsi da karar da mahukuntar fadar suka shigar

- Mahukuntar fadar Kano sun yi karar Gwamna Abdullahi Ganduje akan kafa sabbin masarautu a jihar

Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni ta yanke hukunci akan karar da ke neman a hana sabbin sarakunan da gwamna Ganduje ya nada gudanar da ayyukansu a jihar.

Justis Ahmed Tijani Gbadamasi na kotun ya yi watsi da karar da wadanda ke da alhakin nada sarakuna a Kano suka shigar.

Mahukuntar fadar Kano sun yi karar Gwamna Abdullahi Ganduje akan kafa sabbin masarautu ajin farko har guda hudu a jihar.

Da farko dai kotun ta amsa ukatar masu karar da ke umurtan gwamnatin jihar Kano, kakakin majalisar dokokin jihar da wasu shida da ake kara da su bar komai ya ci gaba da kasance a yadda yake har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar.

KU KARANTA KUMA: Gbajabiamila ya gargadi magatakardar majalisa yayinda batatun lasifiku suka kawo tsaiko a zaman farko

Gwamnatin jihar Kano dai ta rantsar da sabbin sarakuna ajin farko a jihar biyo bayan kaddamar da wata doka, na kafa sabbin masarautu hudu a jihar wanda majalisar dokokin jihar ta gabatar kuma gwamnan jihar ya sanya mata hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel