Gbajabiamila ya gargadi magatakardar majalisa yayinda batatun lasifiku suka kawo tsaiko a zaman farko

Gbajabiamila ya gargadi magatakardar majalisa yayinda batatun lasifiku suka kawo tsaiko a zaman farko

- Zaman majalisar wakilai na farko ya hadu da tsaiko bayan lasifikun majalisar ciki harda na kakakinta sun samu matsala

- Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya gargadi magatakardar majalisa akan ya kafa tawagar da za su dunga tabbatar da daidaitar komai a kullun kafin zamansu

- Gbajabiamila ya gudanar da aikinsa na farko a majalisar inda ya rantsar da Musa Sarki-Adar (APC-Sokoto)

Femi Gbajiabiamila, kakakin majalisar wakilai ya kasance a tsaka mai wuya a lokacin da lasifikan taburin shi ya ki aiki har kusan awa daya a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni a zaman majalisan na farko.

Gbajabiamila zai rantsar da Musa Sarki-Adar (APC-Sokoto), mamban da ya bai samu halartar bikin rantsarwa ba a ranar Talata, kuma magatakardar majalisa, Patrick Giwa, ne ya kamata ya shirya rantsarwar amman sai aka samu jinkiri yayin da ma’aikatan fasaha suka yi kokarin gyaran lasifiku masu matsala.

Daga bisani sai kakakin majalisar ya bukaci magatakardar majalisa da ya kafa wasu mambobi na ma’aikata da za su dunga duba dukkanin lasifikun a kullun kafin a fara zaman majalisar.

Bayan an kammala gyaran lasifikarsa, sai ya gabatar da jawabin gargadi ga magatakardar majalisar.

Yace: “Dan Allah, saboda ci gaba, ya zama dole magatakardar majalisar ya kafa wasu tawaga domin hakkin da ya rataya a wuyansa na tabbatar da komai ya tafi daidai kaama daga lasifika, wutar lantarki, da na’urar sanyaya daki kafin mambobin majalisar su shigo zauren domin kada a sake fuskantar irin haka"

Yayinda aka gyara lasifikar kakakin majalisar, wasu lasifu kalilan ne suke aiki a bangarori biyu na majalisar inda mambobi suka bazama a zauren domin neman masu aiki da za su yi amfani da su.

Sauran layi biyun sun kasance babu lasifiku masu aiki.

Daily Independence ta tattaro cewa kulawa da kayan majalisan baya a hannun magatakardar majalisar wakilai, ya kasance a hannun magatakardar majalisan dokokin kasa, Mohammed Ataba Sani Omolori ne.

Kakakin majalisan ya gudanar da aikin sa na farko, wanda ya kasance rantsar da Sarki-Arda.

KU KARANTA KUMA: Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinawa shugaba Buhari a kokarin da yake na yaki da cin hanci

Har ila yau ya umurci magatakardar da ya sanar da shugaban kasa, shugaban majalisan dattawa da kuma sakataren Gwamnatin Tarayyan Najeriya cewa majalisan ta zabi Femi Gbajabiamila da Idris Wase a matsayin wadanda za su jagoranci majalisar kuma suna jiran karban umurninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel