Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta kwace kujeran sanata APC, David Umaru

Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta kwace kujeran sanata APC, David Umaru

- Kurunkus, kotun kolin Najeriya ta raba gaddama

- Sanata David Umaru ya ga samu, ya ga rashi

- An alanta Mohammad Sani Musa matsayin sahihin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC

Labarin da ke shigowa daga kotun kolin Najeriya da duminsa na nuna cewa kotun a yau Juma'a, 14 ga Yunin 2019 ta kwace kujeran sanatan APC mai wakiltan jihar Neja ta gabas, David Umaru. Ta alanta Mohammad Sani Musa matsayin zakaran zaben.

Kotun kolin ta yi watsi da shari'ar kotun daukaka kara na ranar 8 ga Afrilu, 2019 wacce ta baiwa David Umaru, nasarar cin zaben fidda gwanin jam'iyyar a jihar Neja.

KU KARANTA: Yanzu na zabi a kirani da 'Fes ledi' ba matar shugaban kasa ba - Aisha Buhari

Kwamitin alkalai biyar da suka zauna kan al'amarin karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Muhammad, sun yi ittifakin cewa jawaban lauyan Mohammad Sani, Wole Olanipekun, gaskiya ne kuma lallai shi yayi nasara a zaben fidda gwani.

Saboda haka, ta tabbatar da shari'ar da Alkaliyar babban kotun tarayya dake Abuja, Folashe Giwa-Ogunbanjo, na cewa Musa ne sahihin dan takarar jam'iyyar APC a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel