Dubunsu ta cika: Jami'an tsaro sunyi ram da wasu yan bindiga a Katsina

Dubunsu ta cika: Jami'an tsaro sunyi ram da wasu yan bindiga a Katsina

-Jami'an tsaro sun fafata da wasu yan bindiga a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina

-An kama wani dan bindiga mai shekaru 70 a kauyen Pauwa na karamar hukamar Kankara.

-Jami'an tsaro sun kashe wani dan bindiga a dajin Dan birgima a Katsina

Jami'an tsaro sun fafata da wasu yan bindiga a kamar hukumar Kankara da ke a Katsina inda aka kashe dan bindiga guda aka kuma kama wasu guda ukuk ciki hada wani tsoho dan shekara 70.

Lamarin ya faru ne da marecen ranar Alhamis 14 ga watan Yuni 2019.

Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya sanar da sunan wanda aka kashe a matsayin Kurma.

Isa ya kuma fadi cewa sunan tsohon da aka kama mai shekaru 70 Bawa Naganda.

KARANTA WANNAN: Sakamakon zaben June 12 na kowacce jiha da dalilin da yasa IBB yayi watsi dashi

Jami'in ya bada labarin afkuwar lamarin kamar haka "A ranar 13 ga watan Yuni 2019 da misalin karfe 11:55 na safe mun samu kiran gaggawa cewa an ga a kalla mutum 100 dauke da makamai kusa da kauyen Pauwa a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina tare da shanun sata guda 50.

"An tura hadakar kungiyar jami'an tsaro na Puff Adder da na Sharan Daji zuwa wajen. Da isar jami'an tsaro wajen sai suka fara gwabzawa da yan ta'addan wanda hakan ya sanya yan ta'addan suka ruga cikin tsaunukan dake dajin Rugu.

"An kama wani Bawa Naganda dan shekara 70 a wajen. Jami'ian sun cigaba da zagaye cikin kauyen daga bisani da suka isa dajin Danbirgima , sai suka ga mutum uku akan babura.

"Sai mutanen da ke kan baburan suka budewa wa jami'an wuta, suka yadda baburan suna kokarin rugawa. Jami'an sun mayar da martani wanda a dalilin haka aka kashe wani mai suna Kurma, sa'annan aka kama wani isah Babai mai shekaru 25 da kuma wani Ali Beti.

"Har yanzu de muna ci gaba da bincike." a cewar shi.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel