Umarninka kawai muke jira - Majalisar dokokin tarayya ta sanar da Shugaba Buhari

Umarninka kawai muke jira - Majalisar dokokin tarayya ta sanar da Shugaba Buhari

- Yayinda tayi zamanta na biyu a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, majalisar dattawa tace a shirye take ta karbi duk wani umurni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Majalisar tace za ta aika wani sako zuwa ga Shugaban kasar ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya

- Sanatocin sun kuma yanke shawarar aika wasikar taya murna ga kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da mataimakin kakakin majalisar wakilai Ahmed Idris Wase a bisa nasara da suka yi

Majalisar dattawa a jiya Alhamis, 13 ga watan Yuni tace a shirye take ta karbi duk wani umurni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majalisar dattawan ta tara wacce tayi zama na biyu a yanzu tace za ta tura wani sako zuwa ga Shugaban kasar ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya.

Majalisar dattawan ta kuma ce za ta aika wani sako zuwa ga Shugaban kasar domin sanar masa cewa majalisar dattawa ta tara ta taru sannan cewa an zabi shugabannin ta, Ahmad Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa, da kuma Ovie Omo-Agege a matsayin mataikain Shugaban majalisar dattawan.

KU KARANTA KUMA: Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Borno

Sanatocin sun kuma yanke shawarar aika wasikar taya murna ga kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da mataimakin kakakin majalisar wakilai Ahmed Idris Wase a bisa nasara da suka yi da kuma sanar masu da zaben Lawan da Omo-Agege.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel