An samu nasarar cafke wani kasurgumin dan fashi da makami a Enugu

An samu nasarar cafke wani kasurgumin dan fashi da makami a Enugu

Rundunar 'Yan sandan Jihar Enugu ta ce ta kama wani kasurgumin dan fashi da makami da ba a bayyana sunansa ba da ya dade yana fitinar mutane unguwanin Holy Ghost da Rail-line a garin Enugu.

Kakakin Rundunar 'Yan sandan Jihar, SP Ebere Amaraizu ne ya bayyana hakan cikin jawabin da ya fitar a ranar Juma'a a Enugu inda ya ce an 'Yan sandan Central Police Station ne suka kama wanda zargi da fashi da makamin ne a ranar 13 ga watan Yuni.

Ya ce 'yan sandan sun kwato wayoyin salula, jakunkuna dauke da kudi da kuma karamar bindiga da wanda ake zargin ya ke amfani da shi wurin firgita wadanda ya ke yi wa fashi.

DUBA WANNAN: Assha: 'Yar majalisa ta sha mari a hannun abokin aikin ta

Amaraizu ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan an sanar da 'yan sandan cewa wanda ake zargin ya yi amfani da bindiga wurin yi wa wani fashin wayar salulansa kirar Infinix.

A cewar Amaraizu, wanda ake zargin mazaunin gida mai lambe 28 ne a Mbanugu Street a Coal Camp a Enugu.

Ya ce wanda ake zargin yana bawa 'yan sanda hadin kai a binciken da su ke yi na miyagun ayyukan da ya kasance ya na aikatawa.

"'Yan sanda sun fara kai sumame wuraren da ake zargin ana aikata laifuka a Holy Ghost da Rail Line da kuma wasu wuraren da masu laifi suke cin karen su ba babaka karkashin shirin Operation Puff Adder," inji shi.

Ya ce za su cigaba da gudanar da hakan ne domin tabbatar da tsaro a jihar.

"Sumamen ya zama dole ne saboda umurnin da Kwamishinan 'Yan sandan Jihar, Mr Suleiman Balarabe ya bayar," kamar yadda NAN ta ruwaito.

Source: Legit

Mailfire view pixel