Kungiyar CAN ta zargi Gwamna Bello da nuna bangaranci wurin nade-naden mukami

Kungiyar CAN ta zargi Gwamna Bello da nuna bangaranci wurin nade-naden mukami

Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani Bello na amince da nadin Alhaji Ahmed Ibrahim Matane a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

Musa Rogo Ibrahim, Farmanen Sakataren Ayyuka na Musamman ya kuma sanar da cewa gwamnan ya amince da nadin Alhaji Ibrahim Balarabe a matsayin shugaban ma'aikata da Hajiya Salamatu Abubakar a matsayin Shugaban Ma'aikata.

Sai dai Kungiyar Mabiya Addinin Kirista ta Najeriya (CAN) reshen jihar ta bayyana cewa an fifita bangare guda wurin nade-naden.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

A jawabin da ya yi wurin taron manema labarai da ya kira jiya Laraba a Minna, Shugaban kungiyar, Rabaran Mathias Echioda ya ce abinda gwamnatin ta aikata "fashi da makami ne a siyasance".

"Muna ganin abinda aka aikata ya yi dai-dai da fashi da makami na siyasa kuma ba za mu amince da hakan ba saboda mun taka muhimmiyar rawa wurin zaben gwamnati mai ci a yanzu.

"Ya da ce mu samu wakilci a manyan-manyan mukamai na gwamnati saboda a rika dama wa da mu wurin tsare-tsare da aiwatar da ayyuka," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel