Masu garkuwa da mutane sun nuna mun kabarin yarana bayan sun karbi N2.5m kudin fansa – Inji wani Alhaji

Masu garkuwa da mutane sun nuna mun kabarin yarana bayan sun karbi N2.5m kudin fansa – Inji wani Alhaji

- Wasu masu garkuwa da mutane da suka sace yara biyu a watan da ya gabata a kauyen Dan-Ali da ke jihar Katsina a jiya Alhamis, sun fada ma iyayensu cewa an kashe yaran

- Yan bindigan sun ce an hallaka yaran ne a wani aiki da rundunar sojin sama suka kaddamar a kansu

- Sun fadi hakan ne bayan sun karbi naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansar yaran

Yan bindigan da suka yi garkuwa da yara biyu a watan da ya gabata a kauyen Dan-Ali da ke jihar Katsina a jiya Alhamis, sun fada ma iyayensu cewa an kashe yaran a lokacin da rundunan sojin sama ta kai hari.

Mahaifinsu yace maimakon a sako su bayan sun karbi kudin fansa naira N2.5 million, yan bindigan sun jagorance shi zuwa kabarurrukan yaransa.

Anyi garkuwa da Anas Idris da Ibrahim Idris da misalin karfe 1:30 na tsakar dare a ranar 27 ga watan Mayu a lokacin da suka kai hari gidan. Yan bindigan sun bukaci naira miliyan Miliyan 20 a matsayin kudin fansa wanda daga baya an bada naira miliyan 2.5.

Mahaifinsu, Alhaji Idris Garba Dan Ali, a wani hiran shi da manema labarai yace: “Naje domin na hadu dasu (Yan bindigan) a kauyen Leletu na karamar Hukumar Dan Musa. Suka ce in jira su na dan lokaci. Bayan dan lokaci kadan, su shida suka zo sannan bayan sun karbi kudin, suka bukaci in fada musu wanda nazo ceto.

KU KARANTA KUMA: Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Borno

“Sai suka fada mani cewa yan kwanaki da suka gabata rundunar sojin sama sun gudanar da aikin tayar da yankin kuma cewa an kashe yarana a harin. Sai suka nemi na bisu domin ganin kabarinsu, amma naki sannan na fada masu cewa tunda an kashe su, na bar komai a hannun Allah kuma Allah ya ji kansu da rahma.”

Wani Jami’in sojin sama wanda yayi magana bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba ya karyata zargin da yan fashin suka yi, na cewa rundunan ce ta kashe yaran a harin da suka kai ma yan fashin a jejin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel