Hukumar kwastam ta garkame buhuhunan shinkafa 2,494 da kayayyakin kimanin N47m (Hotuna)

Hukumar kwastam ta garkame buhuhunan shinkafa 2,494 da kayayyakin kimanin N47m (Hotuna)

Rundunar Kwantrola janar na hukumar kwastam shiyar Zone 'A' ta yi arangama da buhuhunan shinkafa 2,494, galolin man gyada 1288 da motocin alfarma na kimanin kudi milyan 47 cikin wata daya.

Mataimakin kwantrolan, DC Yahaya Biu, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Alhamis, 14 ga watan Yuni, 2019.

Yahaya Biu ya kara da cewa an damke wadanda kayayyaki ne a wurare daban-daban na jihar Legas, Ogun da Oyo.

Hukumar kwastam ta garkame buhuhunan shinkafa 2,494 da kayayyakin kimanin N47m (Hotuna)

Hukumar kwastam ta garkame buhuhunan shinkafa 2,494 da kayayyakin kimanin N47m (Hotuna)
Source: Facebook

KU KARANTA: Sakamakon zaben June 12 na kowacce jiha da dalilin da yasa IBB yayi watsi dashi

Yace: "An dauko wadannan kayan ne cikin motoci daban-daban irinsu kirar Mazda, Toyota kimanin shida, manyan motoci biyar da tireloli biyar.

"Motocin suna jibge da kayayyakin kuma an ajiyesu a kwalejin horon hukumar Kwastam da wajen ajiyar Ikeja a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, 2019,"

"Sauran abubuwan da aka kwato ya hada da tirela da motocin bas biyar cike da shinkafa wadda aka kama a unguwar Igbora na jihar Oyo, yayinda aka kama motocin biyar dauke da shinkafa a Idiroko a yankin Ogun."

"Bugu da kari, an damke tirela dauke da galolin man gyada 1,000 da aka shigo dasu daga kasar Malaysiya. An damke tirelan ne a jihar Legas."

Saboda haka, DC Yahaya Biu ya yi kira ga yan fasa kwabri su yi kasuwanci na kwarai kuma su daina sanya rayukan yan Najeriya cikin hadari ta hanyar shigo da lalatattun kayayyakin abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel