Wata kungiya ta bukaci a binciki Obasanjo da Jonathan

Wata kungiya ta bukaci a binciki Obasanjo da Jonathan

- Wata kungiyar gamayya ta najeriya ta bukaci a dakatar da Obasanjo da Jonathan daga halartar kowane taro na kasa

-Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike akan yadda aka kashe kudaden Najeriya tun daga 1999-2015

-Kungiyar ta ce idan gwamnati bata binciki Obasanjo da Jonathan ba to zata dauka cewa bakinsu daya wajen cutatawa yan kasa

kungiyar gamayya ta Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta binciki kuma ta hana tsohon shugaban kasa Obasanjo da Jonathan daga halartar kowanne taro na kasa.

Kungiyar ta ce wannan ya zama dole don a magance barnar da tsofaffin shuwagabannin suka yima kasa.

A wani jawabi da mai gayya mai iko na kungiyar Patriot Sabo Odeh ya sanyawa hannu, kungiyar ta bukaci Muhammadu Buhari ya binciki tsofaffin shuwagabannin biyu sabida ta'asar da sukayi don su fuskanci hukunci.

KARANTA WANNAN: Tsaro: Kungiyar 'yan wasan kwaikwayo ta kai wa Buratai ziyara ta musamman (Hotuna)

Jawabin na cewa kamar haka "Abin ya ta'azzara kasancewar akwai mugayen mutane da dimukaradiyyar kasar nan tasha wahala a hannunsu, wanda bakar niyyarsu ta wulakantar da shekaru 20 na dimukaradiyya. Bakar niyyar ta su ta fito karara inda suke nuna bacin ransu ganin kasar nan ta dauki hanyar gyara duk da bakaken ayyukan da sukayi ma kasar a baya."

"A sabida haka wannan gamayya ta Najeriya na gabatar da kudirorinta guda bakwai zuwa ga gwamnatin tarayya wanda dole a biya mata su don a tabbatar mata da cewa wanna gwamnatin bata hada kai da Obasanjo da Jonathan ba wajen tsotse kasar nan. Bukatun mu sune kamar haka:

"Gwamnatin tarayya ta kaddamar da binciken kudaden da aka kashe tun daga shekarar 1999-2015. A yi wannan bincike da zummar gano asarar da Najeria tayi na albarkatun ta don gano wadanda suka sace kudaden yanzu kuma suke ikirarin sune dattawan kasa.

"Duk wanda ake zarginsa da laifi wajen aikata wannan ta'asa, to ya fuskanci shari'a kuma a yanke mashi hukunci mafi tsanani. idan aka tabbatar da zargin.

"Kuma daga yanzu gwamnatin tarayya kada ta sake aikawa tsohon shugaban kasa Obasanjo da Jonathan kowane goron gayyata zuwa taro na kasa dalilin yin amfani da sukayi da ofishinsu a baya don azurta kasu da iyalansu ta hanyar yiwa yan kasa barna."

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel