Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Borno

Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Borno

- Rahoto ya nuna cewa yan ta’adda sun kai mamaya sansanin sojoji a arewa maso gabas

- An tattaro cewa majiyoyin tsaro sun ce yan bindiga a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, sun far ma sansanin sojin Najeriya a kauyen Kareto a arewa maso gabashin jihar Borno

- Shugaba Buhari a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, ya bayyana cewa Najeriya na shawo kan matsalolin tsaro da tarin taimako da take ba hukumomin tsaro

Yan ta’addan Boko Haram sun kai mamaya wani sansanin sojin Najeriya a yankin arewa maso gabashin kasar inda suka kashe akalla kwamandan soji, inda sauran sojojin suka tsare, wasu majiyoyin tsaro na yan Najeriya biyu suka bayyana hakan a ranar Alhamis.

Legit.ng ta rahoto cewa wasu majiyoyi na tsaro sun bayyana cewa a ranar Laraba yan bindiga sun far ma sansanin sojoji a kauye Kareto da ke arewa maso gabshin jihar Borno, kimomita 130 daga Maiduguri, babbar birnin jihar.

Babu sauran bayanai game da ko an samu Karin mutanen da suka mutu.

Sai dai kuma kakakin rundunar sojin bai yi martan akan lamarin ba zuwa yanzu.

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni ta bayyana cewa yaki da suka da yan Boko Haram na samun gagarumin ci gaba; cewa guggubin yan ta’addan kadan ne suka rage.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a jihar Neja

Sai dai babu wani bayani da ke nuna ko maharan na da alaka da yan Boko Haram ko kuma ISWAP.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jawabin karban aikinsa karo na biyu a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, yace Najeriya na shawo kan matsalolin tsaro da tarin taimako da take ba hukumomin tsaro ta bangaren kudi, kayayyaki da kuma ingantacciyar dabaru na gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel