Yanzu na zabi a kirani da 'Fes ledi' ba matar shugaban kasa ba - Aisha Buhari

Yanzu na zabi a kirani da 'Fes ledi' ba matar shugaban kasa ba - Aisha Buhari

- Aisha Buhari ta ce ita ta bukaci da a kirata da mai dakin shugaban kasa a can baya wanda hakan ya kawo rudani akan yadda za a rika kiran matan gwamnoni

- Aisha Buhari ta bukaci da a rika kiranta da Fes Ledi daga yanzu

- Daga bisani kuma ta roki matan gwamnonin da su yi mata afuwa kan rudanin da ta janyo

Shekara hudu bayan da Muhammadu Buhari yace matarshi bazata rike ofishin Fes ledi ba, Aisha Buhari matar tasa, a ranar Alhamis ta bukaci da a kirata da Fes ledi.

Tun bayan da aka rantsar da Shugaba Buhari karo na farko a matsayin shugaban kasar Najeria, ana kiran mai dakin nasa da matar shugaban kasa.

Amma matar tashi Aisha ta ce daga yanzu mukamin nata ya koma Fes ledi. Ta ce wannan zai magance rudanin da aka sanyawa matan gwamnoni game da mukamin da suke dashi a jihohinsu.

Aisha ta bayyana hakan ne a taron da aka yi a dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa inda aka baiwa matan gwamnoni na da da na yazu kyautar girmamawa.

KARANTA WANNAN: Murtala: Murtala: Ya sanar da kotu cewa wallahi ba zai saki matarsa ba har sai ta biyashi sadakin naira miliyan 3.5 din shi

Ta ce "A lokacin da aka zabi mijina karo na farko, ni na bukaci da a kirani da matar shugaban kasa."

"Amma na lura cewa hakan ya kawo rudani dangane da yadda za a rinka kiran matan gwamnoni a jihohinsu."

"Sabida haka ina rokon ku gafara dangane da rudanin da na kawo, amma yanzu na zabi da a kirani da Fes Ledi." a cewarta.

Wannan matsayar ta matar shugaban kasa ya sabawa alkawarin da shugaba Buhari yayi a 2014 lokacin da yake takara, na cewa ba za ayi ofishin Fes Ledi a gwamnatinsa ba.

a wata hira da buhari yayi da jaridar weekly Trust a cikin watan Satumba 2014, ya ce wannan ofishin na Fes Ledi babu shi a kundin tsarin mulki kuma ya kamata a bari ministirin mata tayi aikin ta ba tare da shiga huruminta ba.

A lokacin ne Aisha Buhari ta bukaci da a kirata da matar shugaban kasa.

Koma de wane suna ake yin amfani da shi, karfin ofishin Aisha Buhari daya yake da na tsofaffin matan shugabannin kasa, a wani rahoto da ICIR ta fitar.

Bugu da kari, yanzu har sunan ana tsammani zai canza.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: -

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel