Murtala: Ya sanar da kotu cewa wallahi ba zai saki matarsa ba har sai ta biyashi sadakin naira miliyan 3.5 din shi

Murtala: Ya sanar da kotu cewa wallahi ba zai saki matarsa ba har sai ta biyashi sadakin naira miliyan 3.5 din shi

- Wani mutumi ya bayyanawa kotu cewar ba zai saki matarsa ba har sai ta biya shi kudin da ya kashe a kanta

- Mutumin ya lissafa duka kudin inda ya bai wa kotu jimillar naira miliyan uku da dubu dari biyar

A jiya Alhamis ne wani hamshakin dan kasuwa, Alhaji Murtala Adamu, ya roki alkalin kotun Gudu akan kada ya amince da bukatar matarsa na raba aurensu, har sai ta dawo mishi da naira miliyan 3.5 da ya kashe a aurenta.

Adamu ya nemi wannan alfarma ne a gurin alkalin a lokacin da ake sauraron karar da matarsa ta kai mai suna Layisatu Abubakar.

Ya ce ba zai taba sakin ta ba har sai ta dawo masa da dukkan kudin da ya kashe a kanta.

Matar ta kai karar ne akan ayi amfani da shari'ar da ta bai wa mace damar raba aurenta da mijinta ta hanyar mai da masa da sadakin da ya bata.

A bayanin da ya yiwa kotu, Adamu ya bayyana cewa matar tasa ta zauna a gidansa na tsawon kwana tara ne kawai bayan yin auren su, inda daga nan ta gudu gidan kawayenta dake garin Jos.

Ya ce sai lokacin da ta fara rashin lafiya ne kawai mahaifiyarta ta kirashi akan ya biya kudin magani.

KU KARANTA: Rikicin masarautar Kano: Ganduje ya bayyana wasu sharudda da Sarki Sanusi zai bi kafin suyi sulhu

A lokacin da yake bayanin, Adamu ya lissafa kudin da ya kashe gaba daya akan matar tasa.

"Ya Mai Shari'a na kashe naira miliyan 1.2 a lokacin bikin mu, wanda ya hada da sadakinta naira dubu tamanin. Na siyo mata kayan sawa irinsu takalma, riguna, atamfa da sarka da dan kunne na naira dubu dari biyar.

"Na kuma biya naira dubu dari bakwai da hamsin na magani lokacin da take rashin lafiya.

"Kafin na yadda na bata takardar ta sai ta dawo mini da dukkanin kudin dana kashe mata," in ji shi.

A bayanin da ta yi, Liyasatu ta bayyanawa kotu cewa ta bar gidan mijin nata bayan kwanaki tara da yin auren ne saboda aljanu suna damunta.

"Duka abubuwan da ya siyo mini suna gidan ban taba ba.

"Bani da kudin da zan iya biyan wannan kudaden da ya bayyana, amma zan iya biyan sadakin dubu tamanin da ya bani," in ji matar.

A karshe alkalin kotun, Ado Mukhtar ya daga karar zuwa ranar 2 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel