Gwamnan Bauchi ya soki masauratun gargajiya kan zaben da ya gabata

Gwamnan Bauchi ya soki masauratun gargajiya kan zaben da ya gabata

- Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya yi suka kan halayyar wasu daga cikin sarakunan gargajiya a lokacin da ake gudanar da manyan zabuka a jihar Bauchi

- Bala Muhammad ya yi kira ga sarakunan da su guji tsoma baki cikin lamuran siyasa, musamman bisa la'akari da cewa sarakuna su na matsayin iyayen al'umma ne

Bala Muhammad, gwamnan jihar Bauchi ya bayyana bacin ransa game da halayyar da wasu daga cikin sarakunan gargajiya a jihar suka nuna lokacin babban zaben da ya gabata.

Muhammad ya yi wannan maganar ne a jiya Alhamis yayin da yake karbar bakoncin sarakunan Misau da Ningi a wata ziyarar ban girma da suka kai masa a fadar gwamnatin jihar Bauchi.

KARANTA KUMA:Jawabin Buhari cike yake karyar abubuwan da ba’ayi ba – PDP

Gwamnan ya fada wa sarakunan cewa, “zai fi kyau idan za suka tsame kansu daga shiga cikin lamuran siyasa, musamman saboda kallon da ake yi masu a matsayin iyayen al’umma.”

Muhammad ya sake jaddada kudurinsa na yin aiki tare da sarakunan domin tabbatar da an samu zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar tasu.

Gwamnan ya cigaba da cewa, gwamnatinsa zata bude gidauniya ta musamman wacce zata kunshi sa hannun sarakunan gargajiya domin shawo kan matsalolin tsaro a yankunansu.

Har wa yau, gwamnan ya yi watsi da batun kirkirar ‘yan sandan jiha inda yake cewa: “ Wannan abu da wasu yan kasar nan ke son a aiwatar ba zai haifar da da mai ido ba face kara tabarbarewar tsaron jihohi.”

A nasa jawabin, Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman ya roki gwamnan da ya kammala titin dake sadarwa zuwa Damban daga Misau domin rage kuncin jama’ar wannan yankin.

A na shi bangaren kuwa, Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya, rokon gwamnan yayi da ya sanya yan asalin yankin Ningi yayin rabon mukaman siyasa tare da bayar da kwangila domin inganta wasu manyan tituna dake cikin biranen jihar. (NAN).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel