Rikicin masarautar Kano: Ganduje ya bayyana wasu sharudda da Sarki Sanusi zai bi kafin suyi sulhu

Rikicin masarautar Kano: Ganduje ya bayyana wasu sharudda da Sarki Sanusi zai bi kafin suyi sulhu

- Gwamnan Kano ya bayyana wasu sharudda da dole sai Sarki Sanusi ya bi kafin su yi sulhu

- Gwamnan ya ce dole Sarkin ya fito ya nemi gafara a gurinsa da kuma al'ummar jihar Kano

- Sannan ya ce dole sai ya fara aikida sabbin masarautu da aka kirkiro

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana wasu sharudda da ya gindayawa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, inda ya bayyana cewa sune kawai matakan da za abi domin tabbatar da sulhu tsakaninsa da Sarki Sanusi.

Gwamnan yayi bayanin hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kwamared Muhammad Garba ya fitar. Sharuddan da gwamnan jihar ya sanyawa Sarkin Kanon, sun hada da batun cewa dole Sarkin Kano ya fito fili ya nemi afuwa a gurin gwamnan da kuma al'ummar jihar Kano baki daya akan wulakanta kimar masarautar da yayi ta hanyar sanya kanshi a harkar siyasa.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a jihar Neja

Haka kuma Gwamnan yayi bayanin cewa, dole sarkin sai yayi mu'amala ta aiki tare da sababbin Sarakuna guda hudu da aka kirkira a matsayinsa na shugabansu.

"Sannan kuma ana bukatar Sarkin yayi amfani da kwarewarsa wajen shugabantar sababbin Sarakunan tare da ganin sun yi ayyukan da ya kamata wurin ciyar da jihar ta Kano gaba ta bangaren zamantakewa da kuma habaka tattalin arziki."

Rikicin Gwamnan Kanon da Sarki Sanusi ya samo asali ne dai tun bayan lokacin da aka kammala zaben gwamna a jihar ta Kano. Inda har yanzu lamarin ke ta faman kwan-gaba kwan-baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel