Kashi 20 cikin 100 na 'yan Najeriya na fama da lalurar tabin hankali - Masana

Kashi 20 cikin 100 na 'yan Najeriya na fama da lalurar tabin hankali - Masana

Fitaccen likitan kwakwalwa da ke aiki a Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, Dakta Aremu Saad ya ce kashi 20 cikin 100 na 'yan Najeriya suna fama da nau'in ciwon hauka daban-daban.

Dakta Aremu ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis yayin da ya ke zantawa da manema labarai kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito.

Ya kuma ce mutane da dama ba su san cewa suna fama da matsalar ba saboda ba su zuwa asibiti yin gwaje-gwaje da ya dace kowa ya rika yi.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: An zabi Abaribe a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa

Ya ce ya samo wannan bayanin ne cikin binciken da masani lafiyar kwakwalwa suka gudanar a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

"Mun kuma tabbatar da cewa kashi 20 cikin 100 na wadanda ke fama da matsalar suna iya zama hatsari ga muatne amma ana iya warke wa idan har mutum ya dage da shan magungunan da likita ya rubuta masa."

Ya ce rashin amincewa da kudirin dokar Lafiyar Kwakwalwa da Majalisar Tarayya ba ta yi ba yana daga cikin abinda ke tsananta matsalar.

Ya ce mutum yana iya kamuwa da ciwon hauka sakamakon shan miyagun kwayoyi, gado, kunshi da damuwa ko kuma idan mutum ya sha kaye a zabe kamar yadda ya faru a Najeriya cikin 'yan kwanakin nan.

Dakta Aremu ya ce yana kyautata zaton majalisa za ta amince da kudin dokar na Lafiyar Kwakwalwa domin hakan zai magance matsalar asibitocin masu fama da hauka da masu aikata laifi da ke ikirarin hauka da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel