Ba banbancin karfi ba ne: Abinda yasa ba a buga kwallo tsakanin maza da maza

Ba banbancin karfi ba ne: Abinda yasa ba a buga kwallo tsakanin maza da maza

Duk mai kallon wasan kwallon kafa ya san cewar ba a buga wani wasan kwallon kafa a matakin duniya tsakanin maza da mata, a kungiyoyin kasashe ko na kulob.

Amma dukkan fitattun kwangiyoyi na kasashe da kulob-kulob da ke duniya na da kungiyoyinsu na mata bayan na maza.

Stephanie Labbe, wata fitacciyar mai tsaron raga a wasan kwallon kafa ce daga kasar Kanada, wacce saboda bajintar da ta nuna ta taba samun gurbi a wata kungiyar kwallon kafa ta maza a kasar Kanada da ke buga wasanni a rukuni na biyu na gasar USL a kasar Amurka.

'Yar wasan na taka rawar gani a kungiyar kafin daga bisani hukumomin da ke kula da gasar su dakatar da ita bisa hujjar cewa gasar USL ta maza ce zalla.

Lebbe da ragowar wasu 'yan wasan kwallon kafa mata irin su Maribel Dominguez, 'yar wasan kasar Argentina da ta taba shiga cikin kungiyar maza kafin ita ma FIFA ta dakatar da ita, sun bayyana cewar ana nuna musu wariyar jinsi ne kawai.

DUBA WANNAN: Masana sun gani tsadar tufafin da Aisha Buhari ta saka yayin bikin ranar dimokradiyya

Duk da akwai sassauci ta fuskar buga wasa a kungiyoyin matasa, FIFA ta ki yarda maza da mata su ke buga wasa tare a wata muhimmiyar gasa a matakin duniya.

Wani masanin harkokin wasanni, Paul Bradley, a jami'ar Moore da ke Liverpool ta kasar Ingila, ya ce wani bincike da ya gudanar a kan wasan kwallon kafa na mata ya gano cewar mata sun fi maza hazaka. Masu bibiyar wasannin kwallon kafa na ganin cewa wasan mata na neman kamo na maza.

"Idan aka yi la'akari da yadda kwarewar wasan mata a 'yan shekarun baya bayan nan, nan da wasu 'yan shekaru masu zuwa muna tsammanin za a sauya alkaluman gwajin jiki," Bradley ya fada wa BBC.

Sannan ya kara da cewa: "musamman idan aka ba su horo a kimiyyar wasanni da karfi da gina jiki da kuma horo na musamman irin wanda ake bawa maza."

Binciken gwajin jiki ya nuna cewar mata sun fi maza saurin gajiya da fiye da kaso 40 a cikin 100, hakan na nufin cewar juriyar namiji ta fi ta mace da kaso 40%.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel