Masana sun gano tsadar tufafin da Aisha Buhari ta saka yayin bikin ranar dimokradiyya

Masana sun gano tsadar tufafin da Aisha Buhari ta saka yayin bikin ranar dimokradiyya

Biyo bayan gutsiri tsomar da ake yi a kan tufafi na salon 'Oscar De La Renta' da matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta saka a bikin ranar dimokradiyya, Legit.ng ta samo wasu muhimman bayanai da zasu bar bakin mai karatu a bude.

Kowa dai ya san Aisha mace ce mai son caba kwalliya da amfani da kayan kawa. A wannan karon ma hakan ce ta faru har ta saka wasu jama'a ke gunaguni.

Tufafi na salon 'Oscar De La Renta' da ke jikin Aisha buhari a wurin taron cin abincin dare na ranar dimokradiyya da aka yi ranar Laraba, ya zama zancen da wasu 'yan Najeriya ke tattauna wa.

Masana sun gani tsadar tufafin da Aisha Buhari ta saka yayin bikin ranar dimokradiyya

Masana sun gani tsadar tufafin da Aisha Buhari ta saka yayin bikin ranar dimokradiyya
Source: Instagram

Abinda ya fi daukan hankali a kan tufafin na 'Osacar De La Renta' masu silke, shine maganar farashinsu da yai dalar Amurka $4,290, kwatankwacin fiye da miliyan N1.5 idan aka juya su zuwa Naira.

DUBA WANNAN: Rikicin Ganduje da Sanusi: Babban basarake a kudu ya ziyarci Obasanjo

Tufafin, da wani kwararre a fannin sanin kwalliyar kayan mata a kasar Amurka, Oscar De La Renta, ya kirkira sun kare a shagunan sayar wa.

Wasu rahoto ya bayyana cewar kafin tufafin su kare a shaguna, farashinsu ya sauko zuwa Dalar kasar Amurka $2,145, fiye da dubu 772 na Naira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel